YAYA AMARYA ZATA GYARA NONON TA ?Rubutawa shafin kowace cuta da maganinta ๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

YAYA AMARYA ZATA GYARA NONON TA ?

Rubutawa shafin kowace cuta da maganinta 

๐Ÿ‘‡๐Ÿ‘‡

To abinda Zaki farayi shine Ki fahimci nononki yaya yake wato shape dinsa da kuma rigarsa ( breziya ) da zakina sakawa. 
Akwai mai mango nono mai Kama da mango. ( shine Wanda kansa yake kallon sama) irin wannan nonon baya zubewa da wuri. Irin wannan bata shan wahalar gyara. sai kuma mikakke ( shine zakuga yana kallon gaba wato ( straight ). 

Gaskiya irin wannan nonon yana saurin faduwa, kuma me wannan ta rinka shan kunun alkama musamman idan sun Fara kwanciyar. 

akwai nono mai kallon gefe zakuga akwai nisa sosai a tsakinin nonuwa Biyu kuma nonon har ya kusa shiga hammata. 

Irin wannan nomon ma yakan Dan kwana Biyu bai zube ba, mai irin wannan nono dole, ta rinka amfani da rigarsa ( breziya ) din da kada kwaba tsakanin Biyu na ( breziya ). 

Amma sauran Kala Biyu na farko zasu Iya amfani da rigar nono Wanda Kawai zatayi musu dai-dai Amma ba'a son mace ta rinka saka rigar nono Wanda ya matse Mata nono saboda zai rinka danne ginshikin nononta kuma daga yayi laushi mako daya sai yazube. 

To dole nononta ya fadi, Ku rinks siyan ( breziya ) mai fadin Hannu da baya saboda yafi hada taimako fiyeda mai siraran Hannu da bashida fadin.

A turawa yan uwa su amfana

pls share and like

Post a Comment

Previous Post Next Post