cincin brodi

**Masha Allah**
*CINCIN BRODI🍞*

Hillani kumatso ga naman bahillashe 🤪💃

*Kayan haɗi*
Flour kofi uku
Yis cokali 2
Madara kofi daya
Sugar cokali 3
Gishiri cokali 1
Kwai 2
Butter rabi

*Procedure*
Kisamu kwano kiba yeast ɗinki dasugar cokali 1,seki dan ɗumama madararki banface me zafi ba (idan kika bari tayi zafi takashe yeast ɗinki ke kika sani 🤣)  kizuba madarar cikin yist da sukarin kirufe zuwa minti 10 don yajiƙa,
Seki dauko flour ki kizuba cikin haɗin yeast ɗinki da ƙwai da narkakkar butter ki kizuba sauran cokali 2 dinki na sukari da gishirinki cokali 1
Sekiyi mixing ɗinsu sosai
Seki samu chopping board ɗinki kokuma kishimfiɗa leda bisa kantarki ki ciro haɗin flour ki ki aza bisa ledar/ board ɗinki kiyita jibgarta eh nace kiyita bugunta har se tayi smooth sannan seki samu kwano kisa haɗin ki rufeshi sosai ki aje cikin rana kokuma wani wuri me zafi har ya kumbura

Wohohooo har naƙagara kigama kibani haƙƙina 😋😋
Idan ya kumbura seki ɗaukoshi kisake bashi kashi sbd iskar dake ciki tafita
Seki dauko tiren gashinki ki cuccura flour ki kanar ƙwalo ki jejjera kirufeshi yasake tashi
Seki gasashi a tsawon minti 20 zuwa 30 a madedeciyar zafi 180° seki shafamashi butter dakin ciroshi daga oven 😋😋 

Zaki iya yinshi as maƙulashe ko breakfast kokuma ( ke ko pillow kikayi da kayanki ke kika sani 🤣)
Masha Allah fulanin gidanga kufito kibiyoni nakawo maku nama

Muntafi jaje akuyar makwafciyata ta ɓata shekaranjiya
Abun Allah nikuma jiya na tsinci akuya bayan layinmu kuzo kutayani murna 🏃‍♀️🏃‍♀️🏃‍♀️

Se mun haɗe 💃💃😘

Post a Comment

Previous Post Next Post