𝗠𝗔𝗦𝗜𝗙𝗔𝗥 𝗗𝗔𝗞𝗘 𝗙𝗔𝗥𝗨𝗪𝗔
𝗚𝗔 𝗦𝗔𝗕𝗕𝗜𝗡 𝗠𝗔'𝗔𝗨𝗥𝗔𝗧𝗔
Kaso 95 daga cikin 100 na matan da sukayi sabon aure suna fuskantar irin wannan matsalar.
Zakuyita soyayya da saurayinki, har kuyi aure cikin girmamawa da farin ciki, amma da lokacin da kukayi aure inba sa'aba yana fara kusantarki, to, zaiyi wahala kuyi sati biyu ko uku ko wata ɗaya baki fara ganin canji daga yadda yake mu'amulantar kiba.
Da yawan maza, da sun gama kwanciyar aure da matansu, shikenan itafa wannan matar batada wata daraja agurinsa, kuma ba lallai taƙara ganin fara'arsaba.
Idan kuwa kika ga yazo yana miki fara'a, to, yanada buƙatarki ne, kuma da zarar ya sami abinda yake nema saiya ƙara ɗaure fuska waishi bayasan a raina shi.
Maza masu irin waɗan-nan ɗabi'un akan samesu da ƙarancin tausayawa matansu, kuma sunada yawan saka mace aikin da yafi ƙarfinta.
Yaku 'ƴan mata ku rinƙa roƙon ALLAH acikin sujadarku ta ko wacce sallah, ta farillah ce ko nafilah, ALLAH ya azurtaku da mijin aure nagari, sannan kuma ku rinƙa sadaka.
Domin kuwa duk kyanki da zarar kin shiga gidan aure, to, shifa daya kusanceki, na sati biyu ko wata ɗaya, to zai daina ganin wannan kyan naki,
Shiyasa Manzon ALLAH {s.a.w} yace: mai addini, kuma mai addininma kuma mai ɗabi'u na ƙwarai.
Waɗanda kuma ke fuskantar irin wannan matsala muna roƙon ALLAH ya cusawa mazansu tausayinsu acikin zuƙatansu.
Sannan ku yawaita istigfar da neman taimakon ALLAH, ku yawaita addu'a musamman acikin sujadarku ta sallah dama dukkan wani gurare da ake amsa addu'ar bayi.
ALLAH ka yaye mana irin wanann masifu dake faruwa ga 'ƴan uwanmu mata Ameen.
ALLAH ka azurta mazan da matan da kyautatawa juna acikin zamantakewarsu Ameen.