HAKIKANIN CUTAR BASUR
wadanda wani lokacin suna samun matsatsi
da talala mai takurasu. A lokacinda suka
samu takurawa da yawa, sai su kumbura
Kumburin wadannan jijiyoyin jini na kara matsi
da takura a garesu cikin dubura. Dalilin
wannan yanayi marar-dadi ga jijiyoyin, sai
kaga wani tsiro ya fito maka a bakin dubura
wanda jijiyar jinince. Zakaji ciwo, ko kai-kayi
koma zubar jini. Wannan lamari shine Malam
Bahaushe ke kira da BASIR-MAI-TSIRO
Wasu daga dalilanda ke haddasa shi sune
kamar haka
1. Gaggawa wajen yin yun'kurin kasaye
abunda dake cikin mutum (kashi). Hakan na
takurama jijiyoyin dubura
2. Yawan zawo(gudawa) ko 'kin fitowar kashi
maisa yawan tsugunni a ban-daki
3. Yawan kiba, musamman wajen mara ko
duwawu
4. Juna-biyu da nakuda (musamman wajen
yunkurin fito da jinjiri daga farji). Yana yima
dubura talala da matsi
5. Jima'i ta dubura (haramun!). Masu jima'i da
iyalansu ta dubura da mafi yawan 'yan luwadi
na fama da basir mai tsiro