Maganin Zazzabi
SHARE 🍀
Naga mutane nata fama da masassara a wannan lokaci saboda yanayin canjin lokaci da aka samu. Amma a haɗo abun sadaka😅
Ga Abubuwan da za'a naima Insha Allahu za'a samu waraka.
1. Kimba ta 100 ta Isa
2.Kanunfari 100
3. Ɗanyar citta (Ginger) ta 100
A hada su waje guda a jajjaga su (Blending) sannan a tafasa su a tukunya, idan ya tafasa sai a sauke ayi surace. Amma kafin ayi suracen a ɗebi kofi daya a sha da zafin sa kamar shayi.
A daure a gwada.
Duk wanda yayi haka ba zai kwana da zazzabi ba, Insha Allahu, zaka iya rabawa 2, kayi sau 2.
Allah yaƙara mana lafiya