*🍂DAGA CIKIN LABARIN NI'IMAR ALJANNA🥰🩶**🍂Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wani

*🍂DAGA CIKIN LABARIN NI'IMAR ALJANNA🥰🩶*

*🍂Manzon Allah (SAW) ya ce: "Wani mutum cikin ƴan aljanna ya nemi izini wajen Allah (SWT) cewa: yana son zai yi noma! Sai Allah ya ce masa: "Kai kuwa me za ka yi da noma? Ashe ba na ba ka duk abin da ka ke buƙata ba?". Sai ya ce: "Gaskiya ne ya Ubangijina. Ka ba ni komai. Amma ni dai in zai yiwu, a ba ni dama in yi noma saboda ina sha'awar hakan". Sai Ubangiji ya ba shi dama. Sai ya je ya yi shuka. Kafin ya ƙifta ido sai shukar ta tsiro ta girma ta yi yabanya har ta kai lokacin girbi. Sai Allah ya ce masa: "Ya kai ɗan Adam! Ga buƙatarka nan an biya maka. Lallai kai ɗan Adam ba wani abu da zai ƙosar da kai" A daidai nan ne sai wani mutumin ƙauye ya ce: "Ya Manzon Allah! Duk yanda aka yi wannan mutumin Baƙuraishe ne ko mutumin Madina! Sune ƴan birni masu dogon buri. Mu mutanen ƙauye ba ruwanmu" Sai Manzon Allah (SAW) ya tuntsure da dariya...*

Post a Comment

Previous Post Next Post