IDAN KARSHEN ZAMANI YAZO!!
Manzo s.a w yace awani hadithi ingantacce, wani zamani zaizo wa al'ummata tsoron Allah zai tafi acikinsu, mutuwar fuji'a ta yawaita, zamani zaizo da za'a dinga yawaita girgizar kasa, zamani zaizo da musulmi baya sallama sai ga Wanda yasani, zamani zaizo da za'a dinga yawaita kisa acikinshi, kuma zamani zaizo da mutane zasu dinga halatta sabo.
Sukace yaushe ne ya manzon Allah!? Yace wannan zaizo ne a karshen zamani, idan kuka ga haka Ku jirayi tashin alqiyama!.
KAMAR ZAMANIMMU NE!!
'Iyaye sun damu da abinci da tufafin yara, amma basu damu da shuka kunya, kima da dabi'u ba acikinsu.
Mutane basu damu da tantancewa acikin nemansu ba halal ne ko haram, sun manta Allah yana yalwata dukiyar halal ya tauye ta haram.
Matashi ko matashiya sukan dauka lokaci mai tsawo wurin wasanni da yawace yawace ko dai a kasuwanni ko wasu wurare amma sugaji a raka'ar farko ta sallah.
Matasa saisu bude kirjinsu don sauraron wakoki, amma inda wa'azi na maganar Allah yazo sai kirjin ya kuntata ta yadda bazai iya karba ba duk wannan sharrin sauraren kida ne.
Mukan cire kudi mai yawa mu sayi abinda ya burge mu da Wanda yabamu sha'awa mai arha ne ko mai tsada, amma alokacin da muka ga akwatin bada sadaka sai mu laluba munemo mafi karanci acikin kudademmu alhalin wannan shine mafi alkhairi akan wadancan!!
Muna zagin juna muna cin mutuncin bayin Allah, mun manta babu mai furta wata magana face raqibu da atidu sun rubuta.
Muna koke gameda yawan hatsari amma muna mantawa da sunnar addu'oin hawa abin hawa da fiyayyen halitta yakoya mana.
Ya Allah ka shiryar damu da zuri'armu kabamu aljannarka madaukakiya amatsayin makoma ta har abada.