BAYANI GAME DA JIKINKU:1_ Shin ko kun san idanuwanku suna kallon duniya ne a kife wato (upside-down) ita kuma kwakwalwa tana aikin gyara hoton.

BAYANI GAME DA JIKINKU:

1_ Shin ko kun san idanuwanku suna kallon duniya ne a kife wato (upside-down) ita kuma kwakwalwa tana aikin gyara hoton.

2_ Shin ko kun san cewa gumi a dabi'ar sa ba shi da wari, sai dai yana samun warin ne idan ya hadu da ragowar kwayoyin cutar bacteria a gangar jiki.

3_ Shin ko kun san idan kuna bacci jin kanshi ku yana daukewa ne gaba daya.

4_ Akwai wani bangare na jikin dan Adam wanda jini baya iya kaiwa gareshi, wato kuryar ido (cornea of the eye).

5_ Mata suna da tsananin jin kamshi da taɓi fiye da maza.

6_ Hancin mutum yana iya tuna kamshi kusan kala 50,000 iri daban daban 

7_ Akwai mil 60.000 (kilomita 96560) na hanyoyin jini a jikin dan adam.

8_ Fiye da rabin kasusuwan jikin mutum suna hannu da kafafu

9_ Mutum yakan kifta ido sau 29 a duk minti daya idan yana magana da wani sannan kuma yana kiftawa sau 4 idan yana karatu.

10_ Hanta tana yin ayyuka 500 a jikin mutum.

11_ Zuciya tana da na'urar wutar lantarki nata, wanda ke iya sanya ta ta buga koda a wajen jiki ne, don haka ba a karkashin kulawar kwakwalwa take gaba daya ba.

12_ Huhu na bangaren dama yana shakar iska fiye da na bangaren hagu

sannan daga karshe kar ka karanta ka wuce, kayi salati ga shugabanmu Annabi Muhammadu (S.A.W).

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post