MATSALAR RASHIN ƊAUKEWAR JININ AL'ADA KO NA HAIHUWA

MATSALAR RASHIN ƊAUKEWAR JININ AL'ADA KO NA HAIHUWA

Wacce jinin al'adarta ko jinin biƙinta yaƙi ɗaukewa bayan lokacin da yakamata ya ɗauke yayi tagwada amfani da wannan haɗin da izinin Allah zai ɗauke.

1- Asamo gayan fura wanda yayi tsami sosai sai a haɗata da gari (kowane iri) sai a dama da ruwan zafi ayi salala sai tasha da zafi zafinsa.
Zatasha sau biyu arana insha Allah jinin zai ɗauke.

2- Asamo gyaɗar miya gongoni ɗaya sai asa ruwa awanke sai azuba ruwa kofi biyu sai abarshi yakwana. Da safe tasha rabin kofi da yamma tasha rabin kofi.

3- Asamo man Tafarnuwa mai kyau tadinga shan chokali biyu safe da rana da dare

4- Asamo garin Babunaj da garin Zaitun da garin Ƙusdul hindi da garin ruman ahaɗasu tadinga ɗiban ƙaramin chokali tasa a ruwan zafi rabin kofi tagauraya tabarshi yajiƙu sai ta tace tasa zuma tasha sau uku arana. Zata iya dafawa kuma.

Allah yasa adace. Ayi Like ayi share  domin wasu su amfana.

@Zauren Abu Muhaisin Islamic & Traditional Herbal and Marriage Counselling.

Post a Comment

Previous Post Next Post