AMFANIN GANYEN BISHIYAR KUKA

AMFANIN GANYEN BISHIYAR KUKA

Ganyen kuka na dauke da sinadarai da dama wadanda ke inganta lafiyar jiki. Wadannan sinadari sun hada da Vitamin C, Vitamin A, Beta Carotene, Potassium, Calcium da dai sauransu.

    Ganyen bishiyar Kuka na inganta lafiya ta hanyoyi da dama, haka kuma ya na magance matsaloli iri-iri da ka iya samun mutum na yau da kullum.

   Ga kadan daga cikin amfanin da Ganyen bishiyar kuka ke da shi:

1. Ya na magance tari da taruwar majina a kirji. 

2. Ya na rage yawan zufa kamar yadda wasu turarukan zamani ke yi.

3. Ya na rage ciwon Asthma da na koda da na  hanta. 

4. Ya na rage gajiya da kumburi.

5. Ya na rage radadin cizon kwari. 

6. Ya na magance tsutsar ciki.

★Wata fa'ida ga mata. 

  Mai son ta kara matsewa sosai ki daka kuka ta yi laushi sosai atankade asamu madara peak milk a hada adama asha. Za ki sha mamaki.
Wannan hadin Amare ma anay musu.

  Amma a kula; busar da ganyen kuka a rana kamar yadda muke yi na rage ma sa sinadarai da akalla kaso 50 cikin dari.
   An fi son a busar a inuwa.

Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

Previous Post Next Post