MENENE RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE?

MENENE RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE?

ABU NA FARKO DAYA KAMATA KI SANI SHINE.

SHI RUWA YANA IYA FITA A GABAN MACE A KOWANNE LOKACI NA RAYUWA.

SABON YARO YANA IYA SAMUN RUWA YANA FITA A GABAN SHI, MATASA SUNA IYA SAMUN RUWA YANA FITA A GABAN SU, MANYA MA HAKA HARDA MATA MA WANDA AL'ADA YA YANKE MUSU.

TO AMMA SHI WANNAN RUWAN MENENE SHI?

RUWAN DAKE ZUBA A GABAN MACE HADUWA NE NA ABUBUWA DABAN DABAN.
 
DAGA CIKI AKWAI RUWAN DAZAI FITO DAGA CIKIN MAHAIFA KANSHI.
SABODA ACIKIN MAHAIFA INDA YARO YAKAN ZAUNA WANI LOKACIN WATA TARA, KODA BABU CIKI SABODA SINADARAN DAKE YAWO AJIKIN MACE.
AKWAI CHANJIN DAKAN FARU ACIKIN MAHAIFA, DAKAN SA RUWA YA DINGA FITOWA DAGA NAN YAZO TA BAKIN MAHAIFA YABI TA GABAN MACE.

BAYAN WANNAN, SAI BAKIN MAHAIFIRAR KANSHI.

CIKIN MAHAIFA SHINE INDA YARO YAKE ZAUNE, BAKIN MAHAIFA KUMA HANYAR DA YARO YAKE FITOWA LOKACIN HAIHUWA.
 
TO BAKIN MAHAIFA SHIMA YANA DA WASU SASSA WANDA SUKE DA DAN WUJI DA YAKAN FITO TA WAJE, WANDA RUWA YANA IYA FITA.
SUMA KUMA SINADARAN DAKE YAWO ACIKIN JININ MACE SUNE SUKAN SAKA WANI LOKACIN YA ZAMA DA YAWA RUWAN, WANI LOKACIN YA ZAMA KADAN, WANI LOKACIN KUMA YA ZAMA BABU SHI KWATA KWATA.

IDAN KUMA AKWAI KWAYOYIN CUTA, AGANSU SUN KARU.

BAYA GA WANNAN KUMA, SAI WASU SASHI NA DAIDAI GABAN MACE.

TA MASHIGAR GABAN MACE AKWAI SUMA WASU SASHI DA SUKE DA DAN HANYA DAN KARAMI DAKE BUDEWA, TASHI HANYAR DA MUKA SANI AKE CEWA GABA.

HAKA NAN SHIMA TA KUSA DA MAFITSARA AKWAI WASU.
HASALI MA SHI WANDA YAKE KUSA DA MAFITSARA, SHINE WANDA AKA SANI MAI KAMA DA ABINDA KESA NAMIJI YA ZUBAR DA RUWA A YAYIN SHA'AWA, TO MACE ITAMA TANA DASHI AKUSA DA MAFITSARAR TA, SAI DAI NATA DAN KARAMI NE.

TO DUKA WADANNAN SUNE SUKE HADUWA SU ZUBA KO KADAN KO DAYAWA KO KUMA YA ZAMANA SUN KAMU DA WASU KWAYOYIN CUTA.

SAI A DINGA GANIN RUWA MAI NAU'I NAU'I KALA KALA.

MUNCE TUN DAGA HAIHUWAR MACE, AKWAI YIWUWAR RUWA YA IYA ZUBA DAGA GABAN TA.

TO MEKE KAWO RUWA YA FITA DAGA GABAN MACE ALOKACIN HAIHUWA?

TUNDA MUN SAN CEWA WATA 9 JINJIRI YANA CIKIN MAHAIFIRAR SA, WANNAN SINADARAN DA MUKAYI MAGANA WANDA KO WACCE MACE SHINE MATANTAKAN TA.

SINADARAI NE KWAYA BIYU.

A KOWANNE WATA, WATO RABIN FARKO NA WATA (KWANA 14 KO ABINDA YAFI HAKA).
AKWAI SINADARIN DA YAKE AKASARI AJIKIN TA.

SU KUMA KWANA 14 NA KARSHE, AKWAI WANI SINADARI SHI KUMA DA YAFI AKASARI AJIKIN TA.

A TSAKIYAN KWANA NA 14 ZUWA NA 16, SHINE WATO AKE CEWA TSAKIYAN WATA.

ALOKACIN MACE TAKE SAKIN KWAI KENAN, WANDA IDAN DA ZATA SADU DA NAMIJI A LOKACIN NAN AKWAI YIWUWAR SAMUN CIKI.

TO WADANNAN SINADARAN GUDA BIYU DA MUKAYI BAYANIN SU, SUNE SUKE BADA NAU'I NAU'I NA RUWA DAKE ZUBA A GABAN MACE.
 
TO A LOKACIN DA MACE KUMA TAKE DA JUNA BIYU WANNAN RUWAN YANA DA YAWA AJIKIN TA.

TUNBA WACCE AKA SAMU WATO PROGESTERONE A SATI BIYU NA KARSHE BA, KAFIN ZUWAN WATA AL'ADA.

HASALI SHI WANNAN PROGESTERONE ABINDA YAKE NUFI WATO (MAI TAIMAKON CIKI) SHINE ABINDA KE SAKA CIKIN MUTUM YA ZAUNA DAIDAI. 
WANDA DA ACE ZA'A SAMU YA ZAMA BASHIDA YAWA, CIKI ZAI IYA ZUBEWA.

TO DUKA WADANNAN ABUBUWAN DA YARO YA ZAMA YA SHIGA CIKIN SU, YA SHIGA CIKIN JININ YARINYA MACE KENAN A LOKACIN DA TAKE CIKI.

TO SHINE ZAI SAKA IDAN AN HAIFI YARINYA, TUNDA AN YANKE CIBI, YANZU BABU HADUWAR JININ TA DA JININ MAHAIFIRAR TA.

TO AMMA KUMA WANDA YA RIGA YA SHIGA CIKIN JININ TA, ZAI IYA YAYI TASIRI AJIKIN TA HAR YA SAKA MAHAIFAR TA DA BAKIN MAHAIFIRAR TA DUK SU SAUKAR DA WANNAN RUWA.

SABODA SINADARAN DA SUKAYI SAURA AJIKIN TA.

TO SHIYASA IDAN KAGA YARO AN HAIFE SHI BAYAN KWANA BIYAR ZUWA KWANA 10.
ANGA RUWA A GABAN MACE, ZA'A GANSHI KUMA MAI DAN KAURI KO MAI RUWA RUWA.

BA WANI ABUN TASHIN HANKALI BANE, WASU YARAN MATA MA HAR JINI AKAN GANI KUMA DUK BA MATSALA BACE BA.

TO DAGA NAN KUMA YARO YA TASHI DAGA JINJIRI HAR ZUWA SHEKARA 7 ZUWA 9.
MAFI YAWANCI A WADANNAN SHEKARUN, SABODA DUK WADANNAN SINADARAN BABU SU AJIKIN BATA FARA ZAMA MACE BA TUKUNNA.

BA DAIDAI BANE AGA RUWA YANA ZUBA A GABAN MACE A WANNAN LOKACI.

DUK LOKACIN DA AKAGA RUWA YA ZUBA A GABAN YARINYA, KO MAI SHAN MAMA, KO MAI RARRAFE KO KUMA WACCE TA FARA ZUWA MAKARANTA BATA KAI SHEKARA 8 BA.

TO ABUNE NA ADUBA SOSAI AGANI MENENE DALILIN DAYA SAKA AKE GANIN RUWA YANA ZUBA A GABANTA.
HASALI MA IDAN HAR AKAGA IRIN WANNAN, ABU NA FARKO DA AKE SO A DUBA KUMA A TANTANCE, A TABBATAR CEWA BASHI BANE.

SHINE KO AKWAI YIWUWAR KO ANA ƁATA TANE.
DUK LOKACIN DAKAJE GURIN LIKITA DA YARINYA MAI IRIN WANNAN SHEKARUN, ABU NA FARKO SHINE ADUBA A GANI BA ANA LALATA TA BANE.

SABODA A WANNAN SHEKARUN YANA DAGA CIKIN MANYAN DALILAN DAYASA YARA YA ZAMA SUNA ZUBAR DA RUWA A GABAN SU.

TO BANDA WANNAN SAI KUMA MUN SAN YARA AKWAI KIRINIYA.

SU SAKA ABU A IDO, SU SAKA ABU A HANCI SU SAKA ABU A BAKI.
TO WANI YARON SABODA KIRINIYA DA SON YASAN KOMAI DA KOMAI, AKWAI YIWUWAR MA ZATA IYA TA SAKA WANI ABU A GABANTA.
 
KILA KO TA TABA GANIN KO BABBA NA AMFANI DA TISSUE PAPER TANA GOGE GABAN TA, ITAMA TACE ZATA GOGE GABAN TA.
TO DAGA NAN KUMA BA TA IYA BANE BA, GARIN GOGE GABA AKWAI YIWUWAR WANNAN TISSUE DIN ZAI IYA YA MAKALE A GABAN TA.

KO KUMA DAN GYADA NE TANA WASA DASHI TA SAKA A GABA, SABODA YARA TUNBA A SHEKARUN IRIN 4,5,6 DIN NAN BA.
SUNA KOKARIN SU SAN KOWANNE SASHI NA JIKIN SU, TO SUNGA ANA RUFE GABA, AMMA SUNA SO SUGA MENENE A GABAN NAN DA AKE RUFEWA.

TO GARIN KOKARIN SU KARA FAHIMTAR GABAN SU, WASU ZASU IYA FITO DA WANI ABU A GABA.

SHIMA YANA DAGA CIKIN BABBAN DALILIN DA YASA AKANGA RUWA A GABAN MACE A WANNAN SHEKARUN.

ACIKIN KALILAN DIN YARA AKWAI WADANDA SUKAN FARA GIRMA ALHALI BASU KAI LOKACIN GIRMA BA.

MAFI YAWANCI KO DAMAN A DANGIN SU SUNADA IRIN WANNAN KO KUMA WASU CUTACE.

SHIYASAA DUK LOKACIN DA AKAGA YARINYA TA FARA NUNA ALAMUN GIRMA, ALHALI BATA KAI SHEKARA 8 BA.
YAKAMATA AJE GURIN LIKITA A DUBA A TANTANCE KO AKWAI MATSALA KO BABU MATSALA.
 
TO IDAN KUMA HAR TAFARA NUNA ALAMUN GIRMA KAFIN SHEKARA 8, WANNAN KWARAI DA GASKE ZA'A IYA AGA RUWA A GABANTA. 

ALLAH YA BAWA DUK WASU MARASA LAFIYA, LAFIYA. 

✍️✍️✍️ Bashir Suraj Adam

Post a Comment

Previous Post Next Post