Karin kumallo wato breakfast yana da matukar amfani ga lafiya, Babu abin alfahari ko birgewa cikin jinkirta wa ko qin yin breakfast da wuri

-------------------------------------------------------------------

Karin kumallo wato breakfast yana da matukar amfani ga lafiya, Babu abin alfahari ko birgewa cikin jinkirta wa ko qin yin breakfast da wuri. 

Wani binkice da aka ɗau shekaru 10 ana yi karshe ya tabbatar da jinkirta yin Breakfast wato daga sanda aka ce karfe 8 na safe ta wuce har zuwa hantsi... Masu aikata hakan na cikin hatsarin kamuwa da ciwon zuciya. Kimanin sama da mutum 998 ne suka kamu da cuttukan zuciya iri daban daban a karshe trial din, kuma cases din yafi yawa a Mata fiye da Maza.

-------------------------------------------------------------------

Don haka adena sake da Breakfast. Musamman a Mata rashin Breakfast nada matukar illa ga jikinku da lafiyar ku.  Infact Rashin Breakfast kan jawo teɓa wato ƙiba mara dalili, da yawa zaka ga Mace chubby amma inka tattauna da ita sai kaji tace ita indan cin abinci ne ai da batai ƙiba ba, bata ma cin abinci sosai... Toh wannan stavation din ne ya jawo.

Zarar karfe 9:00 na safe ta wuce baka ci komi ba toh karma ka dauka Break fast zakai nan gaba. Anso breakfast kar ya wuce 7:30 yai nisa 8:00am.

-------------------------------------------------------------------

Sannan ade cikin binkicen aka kuma gano cin abinci bayan karfe 8 na dare... shima hatsari ne. duk qarin awa guda daga 8pm in mutum yaci abinci to yana qara saka kansa cikin hatsarin kamuwa da larurar  shanyewar ɓarin jiki a dalilin stroke! Wato mutum ka iya samun paralysis. 

Saboda haka a kiyaye.

Post a Comment

Previous Post Next Post