RÃYUWAR BAZAWARI DA BAZAWARA.══════ ❁✿❁ ═══════Rãyuwar Bazawari da Bazawara Tãfi Ta Gwaurãye da Tuzurai Hatsari. Domin Amfi Sãmun Zãrarru da Fitsãrarru Acikin Su..Duk Wanda Suka Taɓa yin Aure, Aka Sãmu Matsala Auren ya Lãlãce, Ko Kuma Matar ta Mutu, Ko Mijin ya Mutu, Wallahi, Tãshin Hankalin da Suke Tsintar Kansu Aciki Yafi Na Gwaurãye da Tuzurai, Musamman Ma 'Ya-Mace,

RÃYUWAR BAZAWARI DA BAZAWARA.
══════ ❁✿❁  ═══════
Rãyuwar Bazawari da Bazawara Tãfi Ta Gwaurãye da Tuzurai Hatsari. Domin Amfi Sãmun Zãrarru da Fitsãrarru Acikin Su.
.
Duk Wanda Suka  Taɓa yin Aure, Aka Sãmu Matsala Auren ya Lãlãce, Ko Kuma Matar ta Mutu, Ko Mijin ya Mutu, Wallahi, Tãshin Hankalin da Suke Tsintar Kansu Aciki Yafi Na Gwaurãye da Tuzurai, Musamman  Ma 'Ya-Mace,
.
Sukanyi Kũkan Ba'kin Ciki, Tãre da Zubda Hawãye, Su Kãsa Bacci, Su Kasa Sãmun Sukũni, Kaga Suna Cin Abinci Amma Suna ta Rãmewa, Sabo da Babu Natsuwar Zũciya A Tare dasu.
.
IYAYE YÃKAMATA KUSAN WANNAN
Bazawara Tana da Buqãtar Kula Fiye da Budurwa, Agurin Iyayenta da Yãyunta, Kãfin Allah ya Haɗa ta da Manemi, Haka Shi Ma Bazawari Matuqar Baida Hãlin yin Wani Auren, Wãjibin Iyaye ne da 'Yan-Uwa Su Tallafa Masa ya Sãmu ya Auri Wata. Don Cēto Su daga Cikin Baqar 'Kaddara.
.
Bazan Ambaci Komai Game da Dũniyarsu ba, Domin Abu ne da Kusan Kõwa ya Sani, Tare da Cewa Dukda Mun San Zãfin Tuntuɓe Amma Wanda Yayi, Shi Kaɗai Yasan Irin Zãfi da Raɗaɗin da Yake Ji.
.
ABIN TAKAICI.
Yadda Iyayenmu Ke Wãtsi da Rãyuwar Bazawara, Babu Kula, In Za'a Bãta Abu Awulaqance Ake Bãta, Wata Ma Iyayenta Bãbu Ruwansu da Cinta da Shanta, Sun Zura Mata Ido Sun barta da  'Kawãyen Banza, Wannan ba 'Karamin Kuskure Bane, Kuma Allah Zai Tambaye ku Akan Hakkinta. Yakamãta Ku Kwan da Sani.
══════ ❁✿❁  ═══════
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺯﻭﺝ ﺍﻟﻌﺰﺍﺏ ﻭﺍﻟﻌﺎﺯﺑﺎﺕ
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺍﻟﻄﻒ ﺑﺎﻟﻤﻄﻠﻘﺎﺕ ﻭﺍﻷﺭﺍﻣﻞ ﻭﺍﻟﻨﺎﺯﺣﺎﺕ ﻭﻛﻞ ﺍﻟﺒﻨﺎﺕ
ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺃﺳﻌﺪ ﺍﻟﻤﺘﺰﻭﺟﻴﻦ ﻭﺍﺭﺯﻗﻬﻢ ﺍﻟﺬﺭﻳﺔ ﺍﻟﺼﺎﻟﺤﺔ.

Post a Comment

Previous Post Next Post