sultan chip

🍋🍋MATA MASU AJI🍋🍋

    🍋 SULTAN CHIP🍋

   Dankali 6
Albasa 2, Tumatir 2
Maggi 2, curry
Tafarnuwa 1
Attarugu 2

   A yanka dankali a soya sama sama a dafa nama da albasa 1 da kayan kamshi idan ya dahu a ajiye ruwan naman gefe daya, a nika naman a yanka albasa, attarugu, tumatir da tafarnuwa. 
   A dora ruwan naman akan wuta, a zuba nikakken naman da yankakken kayan miya tare da soyayyan dankali, Maggi gishiri da Curry yanda zasu isa. Abari su dahu minti 10_15 harsai ruwan ya tsotse. 

Post a Comment

Previous Post Next Post