AMFANIN YADIYA A JIKIN DAN ADAMSharadin shine ayi Sharing 👉👉

AMFANIN YADIYA A JIKIN DAN ADAM

Sharadin shine ayi Sharing 👉👉

Yadiya tana daya daga cikin abinci hausawa na gargajiya, ana dafata ne a kwada da yaji tare da sauran kayan hadi, sanna aci.
To ba iya nan yadiya ta tsaya ba, tana magance wasu cututtuka da ke addabar al'umma, ga kadan daga cikin irin cututtukan da take magancewa;-

                   MAGANIN SANYIN KASHI
                   
Asamu saiwar yadiya da saiwar zogale adafa atace arika shan kofi daya sau biyu arana zuwa kwana tara.

                       MAGANIN ZAZZABI
                      
Adafa ganyen yadiya atace azuba zuma agarwaya asha kofi daya sau biyu arana zuwa kwana uku.

             MAGANIN GYANBO KO RAUNI
             
Adaka ganyen yadiya atankade, arika barbadawa akan gyanbo ko rauni bayan an wanke gyanbon ko raunin.

       MAGANIN CIWON SUGA

Asamu saiwar yadiya da ganyen garahunu da sassaken tsamiya da ganyen mangoro da ganyen zogale.
Adaka atankade atafasa cokali biyu acikin ruwa kofi daya atace arika shan kofi daya sau biyu arana zuwa kwana 14.

              MAGANIN NI'IMA NA MATA
              
Asamu saiwar yadiya da sassaken baure da Kanumfari adafa atace azuba mazar kwaila agarwaya asha kofi daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

                   DON SAUKAKA HAIHUWA
                    
Mata masu ciki kan iya dafa ganyen yadiya su tace su rika shan kofi daya sau biyu arana har zuwa lokacin haihuwa. Insha'Allahu zasu haihu lafiya da yardar Allah.

                 MAGANIN KARFIN MAZA
                 
Asamu saiwar yadiya da saiwar kargo(kalgo) da saiwar hankufa da saiwar bagaruwa.
Adafa atace azuba zuma agarwaya asha rabin kofi sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

        MAGANIN CIWON MARA NA MATA
       
Asamu saiwar yadiya da jar kanwa 'yar kadan adafa atace arika shan kofi daya sau biyu arana zuwa kwana bakwai.

Ku yi Following page ɗina ta hanyar danna bulun Rubutun dake kasa 👇👇

Malama Juwairiyya Bintu Outhman 

Allah yasa mudace

Post a Comment

Previous Post Next Post