KINSAN AMFANIN DA KANUNFARI KEYI A JIKIN MACE..?
Kamar yanda mata ke ajiye Zuma a gida haka yanzu mata basa rabuwa da kanunfari domin duk wani hadin daka na musamman ko hadin ruwan jaraba ko wani tsumi idan kuka bincika zakuga akwai sa hannun kanunfari don haka kema ki ajiye shi don burge mijinki. .
Duk lokacinda zaki dafa shayi kada kimanta dashi domin
idan ya hadu da lefton yana aiki a jikin mace wajen karin ni'ima kuma ya na da kyau yajinki ya zama akwai kunfari aciki
Ana Amfani da kanimfari wajen rage tumbi ki jika shi aruwa idan ya yini ajike sai kishanye ruwan ki kara wani zaki ga cikin ki ya saki kinyi bayan gida wannan shine alamar yayi miki aiki
Ana Amfani da Kanimfari wajen maganin infection idan kika saka ruwa tafasashe a flast sai ki zuba shi aciki da ganyen magarya kirufe sai yayi kamar sa'a daya (1 hour) zaki yini kina yin tsarki dashi har zuwa dare. Zaki iya daka garin kanimfari ki hadashi da totuwar raken
dakika sha yabushe sai ki sami farin muski (miskul dahra) ki cakuda shi sosai da garin da totuwar raken da kuma muskin idan ya bushe sai ki ringa turaren tsugunawa dashi wannan kada ki barshi.
ku jaraba kusha mamaki
A kuma turawa yan uwa domin suma su amfana
AYA,DABINO DA KWAKWA
Aya misalin yawan gwangwanin madara ta peak guda,dabino ka cika hannunka na dama a matsayin ma'auni,kwakwa qwallo daya zaka fashe sai kayi blending nasu ka tace ka sha cup daya a kullum , kada ka sa sugar kada ka sa Zuma kada ka sa madara kada ka sa flavour, ka sha a yanda ka hada natural drinks ne very healthy.
Na siyarwa baya da garanti domin kayan flavour da zaqi ne suke saka mashi wanda illa ce,ka da ka kara komai a ciki Dan haka ka hada da kanka ko ka sa matarka ta hada maka.
Amfaninsa
1.Neman karfin sha'awa
2.Samun ruwan maniyi
3.Maganin kasala da yawan gajiya.
4.Maganin rama wacce bata dalilin ciwo ko jinya ba.
5.Karfin jiki da kuzari.
6.Maganin zafin ciki da tashin zuciya.
7.Maganin rashin cin abinci
8.Masu low sperm count da motility
9.Wankin ciki daga cushewa
10.Karin ni'ima ga mace mai bushewar gaba
11. Mace mai shayarwa zata samu ruwan nono mai yawa mai lafiya.
12.Namiji ya sha bayan an kammale saduwa nan take za a maida abunda ya zuba.
13.Mai neman karfin kokolwa ya zanka sha zai yi mamaki.
14.Mai neman jini da ruwan jiki masu lafiya.
15.Namijin da ke shirin yin aure ya zanka sha kullum wata biyu kamin auren zai yi mamaki idan an yi aure domin da yardar Allah za a yi saurin samun juna biyu.
16.Samun bacci da hutu mai dadi a jiki.
Wallahi wannan yafi a sha maltina ko cocacola,ko duk wani kayan sha na zaqi na roba kona kolba.
Masu Neman magani garanti a nememu wlhy zaku yaba zaku gode ba cuta ba cutarwa.