Bayan ya lakaɗa mata duka, ya ci mutuncinta. Ta kalle shi ta ce: Zan je in kai ƙararka.

Bayan ya lakaɗa mata duka, ya ci mutuncinta. Ta kalle shi ta ce: Zan je in kai ƙararka. 

Ya ce: ba sai kin fita ba, babu in da zan barki ki je.

Ta tashi ta nufi banɗaki, ta yi alwala, ta fara Sallar Nafila, ta yi doguwar sujjada, tana  addu'a. Bayan sallamewarta, sai ta sake ɗaga hannu don ci gaba da addu'a.
Kwatsam Mijin ya riƙe hannayenta, yanzu duk ƙarar da ki ka kai a Sujjada bata isa ba sai kin sake ɗaga hannu. Don Allah ki yi haƙuri, wallahi duk abin da na aikata ya faru ne a cikin fushi, wallahi na yi miki alƙawarin ba zan sake ba.

Ta kalle shi cikin murmushi, ta ce: da ka ƙyale ni na cigaba da addu'a ta, wallahi tun da na sanya kaina a cikin Sujjada babu wani alheri face sai da na roƙi Allah ya baka.

Tare da duk abin da kake aikatawa, kai Mijina ne, kuma ina ƙaunarka sosai,  ya za a yi na yi maka mummunar addu'a...!?

Post a Comment

Previous Post Next Post