Assalamu Alaikum Warahamatullahi Uwargida da fatan kina cikin koshin lafiya da farin ciki Allah yasa haka amin. A yau na kawo muku yadda ake yin Pazza da kuma kayan hadi a shakaratu lafiya.
Kayan hadi
· Filawa
· Gishiri
· Yis
· Man zaitun
· Manshanun kanti (Cheese)
· Mayonnaise
· Kayan kamshi
· Tumatir da farar albasa da koren tattasai
· Tsokar kaza
Yadda ake yi:-
Da farko za a jika yis da ruwan dumi kamar tsawon minti 10, sai ki zuba gishiri da man zaitun. Sannan sai ki kara filawa a cikin wannan ruwan yis din ki kwaba har sai ya yi tauri. Idan ma kika ji shi ya yi ruwa ko lauashi sosai sai ki kara fulawa don yayi tauri.
Daga nan sai ki rufe ki bar shi ya hau zuwa mintina 30. Idan ya hau (kumbura) sai ki sami farantin gashi ki juye filawar a ciki sannan ki sanya a cikin oben ki gasa ki bar shi tsawon mintuna biyar.
Ana sai ki yanka tumatir da farar albasa da koren tattasai kanana. Sai ki koma wurin fulawarki ki duba idan ta gasu sai ki fito da ita. Sannan ki dauko kayan tumatir din da kika yanka sai ki zuzzuba akai da dan garin kayan kamshi ki barbada. Sai ki sami tsokar naman kazarki da kika yanka kanana tare ki zuzzuba akai.
Tags:
food