HANYOYIN GYARAN JIKI

HANYOYIN GYARAN JIKI

 

Ina amarya da uwargida masuson burge oga da sallah idan kika bi wannan matakan na gyaran jiki cikin kwana ashirin zaki chanza
 

1.lalle zaki kwaba lalle zalla sai ki shafe jikinki dashi

2.alkama ki kwabata da madara da zuma sai ki shafa kan lallen inya bushe ki murje

3.dilka sai ki kwaba dilka da ruwan xafi ki shafa

4.hayakin gab gab sai kiyi hayaki da gab gab duk jikinki sai ki nemi man xaitun ki dangwala kina murje dilkar da ita

5.kurkur lemontsami kwai madara ki kwaba ki kara murje jikinki dashi

6.wanka da ruwan lalle ruwan da kika jika lalle dashi xalla

7.sai ki nemi haddadden ko na dilka sabulunki ki wanke jikinki banda soso

8.sai ki xuba madarar turare kamar kala uku aruwa ki dauraye jkinki dashi kibarshi ya bushe

9.sai ki nemi icen dorot ki yi hayakinshi ki maimaita hakan akullum harxuwa kwana ashirin ko fiye keda kanki sai kin birge kanki balle nakusa dake sannan ki rage shiga rana ko inxaki fita kisa safa da nikab

 

FARAR HUMRA

 

garin humra(fari)
mahala
hawi
lubban
misik
turaren mena
turaren ambar
madarar turaren lexus
madarar turaren sandol
zaki jika ko ki tafasa garin humra tare da dakakken hawi,mahala,lubban da misik ki barshi ya kwana sai ki zuba turarukanki ki motsa ki rufe bayan kwana biyu ki bude ki kara turare har sati1 sai ki tsiyaye ko ki tace ki zuba cikin kwalbarki kike shafawa yana kama jiki sosai.
 

BAKAR HUMRA
yadda xaki hada farar haka xaki hadata sede xaki iya canxa wasu kalolin madarar turaren

 

KAMSHIN JIKI

 

turaren amarya
turaren duro
garin sandol
farce
turare dan goma
itacen daro
ki wanke farce ki shanya sai ki soya ki daka ki tankade sai ki kwaba da turaren amarya kisa garin sandol da garin icen daro sai ki xuba sauran turarukan ki kwaba ki rika shafawa yana kama jiki

 

· 
KULACCA

 

body lotion
misik na roba
garin ambar
humra
madarar turaren da kikeso kala5
ki daka humra da ambar suyi laushi sai ki hadesu da turarukanki ki gauraya da lotion ki rufe yay awa uku sai ki fara amfani dashi.

itacen sandol
garin ambar
turaren ambar
turaren sandol rose
zaki tafasa sandol da ambar sai ki zuba sauran turarukan idan ya huce ki juye duk sanda zakuyi wanka ki duba cikin ruwan wanka zakiga yadda kamshi zai kama jikinki.

 

KURKUR(TUMERIC)

 

kamar yadda kuka sani ana amfani da Kurkur wajen GIRKI da kuma GYARAN JIKI. 
bari mudau gyaran jiki, A nijeria kabilar kanuri da shuwa su sukafi amfani dashi wajen gyaran amare don su sami fata mai laushi da haske sannan kurkur yana magance kuraje (pimples),kaushin fata,kyasbi da kuma tabo. saboda haka zan koya muku hadin kurkur wanda zaisa fatar ku haske da kuma laushi(haske bana blicing ba)..

1.kurkur
lemon tsami
gurji
nono ko madara
zaki markada gurji sai ki matsa lemon tsami ki zuba madara da kurkur sai ki kwaba su hadu sannan ki shafa duka jikinki ya samu karmar awa daya sai ki wanke kiyi kamar na sati daya zakiga canji
 

2.zaki iya kwaba kurkur da madara da kwai ki rika shafawa sau biyu arana don samun hasken fata
 

3.kurkur
man zaitun
madara da lemon tsami
ki hadesu ki kwaba sai ki rinkg shafawa a fuska kamar minti talatin sai ki wanke kiyi kamar sati biyu kinayi kullum.

 

GYARAN FATA

 

1.lalle
kwai
gishiri
kurkur
zaki fasa kwai kisa gishiri kisa lalle ki kadasu sosai kisa kurkur ki tuka idan zaki kwanta sai ki shafa da safe kiyi wanka yana magance kananun kuraje

garin lalle
garin dalbejiya
kurkur
sabulun gana
ki cakudasu da sabulun gana sai ki shafa a fuska bayan minti ashirin ki wanke fuskarki zatayi fresh

ya'yan auduga
man zogale
man shanu
kurkur
farar wuta
zaki hada ya'yan auduga,man zogale,man shanu,kurkur ki soyasu sama sama idan ya huce sai kisa dakakken farar wuta, sai ki tace,ki rinka shafawa idan zaki kwanta

man ridi
man kadanya
sabulun salo
zaki tafasasu sai kisa gishiri kadan idan ya huce sai ki shafe a jikinki har fuskarki idan ya kai minti ashirin sai kiyi wanka. yana gyara fata sosai

 

GYARAN FATA

1.hadin sabulu
sabulun salo
sabulun gana
lemon tsami
bawon kwai
kurkur
dilka
ki kirbesu gabadaya ki dinga wanka dashi yana gyara fata

bawon kwai
gishiri
sabulun salo
sabulun gana
sabulun habba
lalle
shima ki kirbeshi kina wanka dashi fatarki zatayi kyau

 

GYARAN JIKI 

madarar ruwa
abarba
kurkum
a hada madarar ruwa da ruwan abarba a shafa a jiki inda ya bushe sai a shafa kwababben kurkum a jiin akan ruwan madarar da ruwan abarbar idan ya bushe sai a murje jiki aje ayi wanka, yana sa kyan jiki, ya yi taushi santsi da kyalli.

GYARAN JIKI 

 

ruwan aloevera
ruwan kankana
ruwan abarba
madarar ruwa
zuma
a hada ruwan abarba da kankana da ruwan aloevra cokali goma goma, da madarar ruwa cokali bakwai zuma da man zaitun cokali uku-uku ki hada ki gauraya su hadu sosai ki shafe duk jikinki da shi har fuskarki idan ya bushe zuwa awa daya ko rabin awa sai ki je kiyi wanka, yana sa kyau fata da laushi da taushi da kyalli
 
SABULUN WANKA NA BAKAR MACE
SABULUN SALO KO SABULUN GHANA

 

majigi
juma
lemon tsami
zaitun

a hada sabulun ghana da majigi a dake a zuba zuma a matsa lemon tsami kadan a saka man zaitun cokali uku, a hada a kwaba, bakar mace da ba ta son tayi fari sai ta dinga wanka da shi, zai sa tayi kyau fatarta tayi taushi da santsi
SABULUN WANKA

Post a Comment

Previous Post Next Post