ABUBUWA GUDA BAKWAI DA KO DA WASA KAR KI BARI SU TABA MIKI FUSKA
Abubuwa guda Bakwai (7) da bai kamata ki bari su ta6a miki fuska ba ko da wasa.
Fuska tana daya daga cikin ababen da suka kamata a kula da su domin da zarar an ga mutum fuska ce abar da za a fara kalla. Mata da dama domin neman gyara sai su shafa ababe da dama domin gyaran fuskarsu ba tare da sanin ko wannan abin ya dace da fuskar ko bai dace da ita ba.
Akwai ababen da in an shafa a fuska maimakon su kawo wa mutum waraka sai su kara feso kuraje a fuskar. Don haka zan lissafo su yanzu domin a yi la’akari.
• Bai kamata idan an zo fesa turaren gashi ya taba fuska ba. Domin idan wannan turaren ya taba fuska yakan janyo gautsin fata da dada yankwanewa ga fuska. Sai a kula.
• Kada a shafa man ‘lotion’ ko wane iri a fuska. Yawan shafa man na toshe ramukan gashi da ke fuska kuma hakan yakan haifar da fesowar kuraje.
• A kula kada a shafa turaren hammata a fuska (deodorant). Kamar yadda ba za a iya daukar tawul din fuska a goge hammata ba, haka bai dace a shafa turaren hammata a fuska ba koda wannan ya kasance mai yawan gumi.
• Man wanke gashi ‘shampoo’ na dauke da sinadaren bata fuska. Don haka, sai a kula idan an zo wanke gashin kai, kada a hada kumfan wajen wanke fuska domin hakan yakan sanya fuska dada yankwanewa da kuma bushewa.
• Idan an zo yin hadin man wanke gashi kamar man ‘mayonnaise’ sai a kula kada ya taba fuska. Idan ya taba fuska, yana hana fatar fuskar numfasawa har ya haifar da fesowar kuraje.
• A kula wajen amfani da nau’o’in launin da ake shafawa a gashi ‘hair dye’ a fuska a matsayin ‘eye shadow.’ Yin hakan na haifar da fesowar kananan kuraje da za su bata fuska.