vegetables macaroni

Assalamu Alaikum uwargida tare da fatar ana cikin koshin lafiya. Allah Yasa! Akwai hanyoyi da dama wadanda ake bi wajen dafa makaroni.
Wadansu suna dafa ta fara da miya, wadansu suna dafa ta da mai da yaji, wadansu kuma suna yin dafa-dukarta.

Dafa-duka ba ta tsaya wajen hada mai da kayan miya waje guda ba, tana da nau’o’i daban-daban, don haka ne a yau na kawo muku sabuwar hanyar dafa-dukar makaroni domin sanya kunnen maigida motsi.

ABUBUWAN DA AKE BUKATA
Makaroni
Nama
Tafarnuwa
Attarugu
Karas
Kori
‘Peas’
Magi
Albasa
Yadda Ake Hadi
A wanke kaza da ruwan kanwa yadda karninta zai fita sannan a dora a tukunya.

Sai a yanka albasa a sa dan gishiri kadan har sai kazar ta yi laushi sosai sannan a sauke ta dan huce.

Bayan haka a nika naman kazar sannan a mulmula shi sai a saka a ruwan kwai sannan a soya a ajiye a gefe.

A dora wata tukunyar a gefe a zuba mata man gyada kadan da yankakkiyar albasa sai a zuba romon kazar a ciki.

Sai a jajjaga attarugu da tafarnuwa kamar dunkule daya a zuba a kai sannan a rufe.

Bayan ya dan tafaso sai a zuba makaroni a ciki.

Sannan a kankare karas a yanka shi kanana a wanke.

A zuba magi da kori a cikin tukunyar.

Idan ruwan ya kusan tsotsewa sai a zuba karas din da ‘peas’ a gauraya da soyayyar kazar a ciki a rage wutar sannan a rufe na tsawon minti biyar, sai a sauke girki ya hadu.

Post a Comment

Previous Post Next Post