Body odour (warin jiki)Mutane dayawa suna fama da wannan matsalar ta warin jiki, duk inda suka wuce sai an to she hanci, wasu kan warin jikin su yana da mun su sosai. Yana yin zufa kadan shikenan sai ya fara wari, koda kuwa ya fito da ga wanka ne yayi zufan. Zufa a asalin sa bai da wari ko kadan, To me yake kawo wannan warin?

Body odour (warin jiki)

Mutane dayawa suna fama da wannan matsalar ta warin jiki, duk inda suka wuce sai an to she hanci, wasu kan warin jikin su yana da mun su sosai. Yana yin zufa kadan shikenan sai ya fara wari, koda kuwa ya fito da ga wanka ne yayi zufan. Zufa a asalin sa bai da wari ko kadan, To me yake kawo wannan warin?

Wasu kwayoyin cututtuka na bacteria da suke fata su suke haifar da wannan warin jiki, in suka hadu da zufa sai su kara yawa su na producing din wari mai tsananin gaske. Shi yasa in mutum yayi dan zufa ko kadan ne sai ya fara wari.. bacterian suna bukan ruwa kafin su habaka shiya sa ko wanka mutum yayi bai bushe da kyau ba, in yasa  kaya can sai dai yaji ya fara wari.

In mutum yana fana da wannan matsalar ba turare ne maganin ba kuma ba shine mafita ba wani lokaci turare sai ya haifar da wani wariwarikamshikamshi da yafi warin wari. Tabbas yana da kyau saka turare amman bai maganin warin jiki zallanshi har sai an hada wasu da ga cikin abubuwan da zan jero a kasa...

👉Na farko dole mutum ya zama yana wanka da kyau, yana kokarin wanke duk wata zufan da yake hammata da tsakankanin cinyoyin sa da duk wani lungu da sakon da yake da gashi a jikin shi.

👉Sai kuma aske gashin Hammata da na tsakanin cinyoyi don kuwa shike rike zufa ya ki bushewa da wuri.

👉Da su iya amfanin da sabulun wanka mai antibacteria don rage wayannan kwayoyin bacteria.

👉Akwai masu matsalar yawan zufa sannan kuma ga warin jiki, suna iya amfani da maganin rage fitan zufa waton antiperspirant  ana shafashi a hammata.

👉A kula da wanki da canza kaya akai akai.
👉Akwai abubuwan da ake ci da yake fita ta zufa ya haifar da wani wari, misali tafarnuwa da albasa. In mutum yana yawan cin su sai ya rage.

👉Rage cin abincin mai yaji don yana sa mutum zufa sosai.

In abu yaci tira yana da kyau a nemi shawaran likitan fata...

Allah ya kara mana lafiya.. Amin.

Post a Comment

Previous Post Next Post