WASU DALILAI DAKE HANA WASU MATAN SAMUN MAZAJEN AURE
Rashin aure da wuri a wannan zamani na daya daga cikin matsalolin da ke ci wa al'ummar mu tuwo a kwarya musamman ma a tsakanin mata wadan da yanzu kan dade basu samu mijin aure ba.
Sai dai duk da alkaluman da ke nuna cewa mata a wannan zamanin na neman su fi maza yawa, masana na ganin akwai wasu dalilai da dama da ke sa matan yin nauyin kasuwa.
ta samu ta tattaro maku wasu daga cikin manyan dalilan da aka fi danganta su da alhakin kawowa matan cikas.
1. Tara samari barkatai : dayawan mata basu fahimchi cewa tara samari barkata ba farin jini bane hasalima kashe kasuwane ga yan mata bama kamar ache akwai samarin banza aciki. Domin duk saurayin kirkin da yake ganinki da mutanen banza bazai taba aurenki ba koda yafara soyayya dake zai gudu ne yabarki da tarin samarinki. Maa zaiyi wahala kaga macen kirki tana tara samari dayawa.
2. Ruwan ido: Wasu matan dai ruwan ido gare su. Za kuji cewa su suna cewa sai mai kudi iri kaza da mota kaza ko gida kaza. Mata kada ku manta da cewa arziki nufin Allah ne. Sannan kutuna cewa ya iyayenku mata suka auri iyayenku maza?.
3. Zurzzurfan karatu: Maza da dama dai na tsoron auren macen da tayi nisa sosai a karatun zamani suna ganin cewa ba za su iya juya ta ba. Wannan dalilin yasa zakaga mafiyawanchin matan da sukayi karatu mai zurfi sukan dade ba aure kuma koda lokachin auren yazo basuchika auren saurayiba zasu sami maimatane su aura.
4. Zafin kishi: Wasu matan suna da zafin kishi shi ne ma ya ke sanyawa kuji sunce ba su son mai mata koda kuwa shi yana da sha'awar auren su. Hakasan saudayawa yakansa mata nadama wanda dayawa idan damar ta kubche zai wahala ta dawo cikin lokachi.
5. Tsadar al'adun aure: A lokuta da dama dai mata da maza dukan su kan dade basu yi aure ba sakamakon tsananin tsadar al'adun da aka likawa auren kamar su kayan daki da lefa da sauran bidi'oi.
6. Sihiri: Wasu matan kan dade a gidajen iyayen su ne ba aure a sanadiyyar sihirin da wasu makiya ko mahassadan su kan yi masu kukuma shigar jinnul ashiq ajikin mache wanda ko mache samu tsayayye zaa rika yawan samun sabani har abin ya lalache.
7. Shigar banza Allah ya halicchi maza datsananin kishi namiji koda mutiman banzane yana bukatar mata tagari duk namijin kirka baya auren mache mai son nuna tsirauchinta ga alumma akoda yaushe tunaninsa tayaya zataba diya sa tarbiyya mai kyau idan ita kanta batada addini ba tarbiyya.?
8. Muamularta Uwarta da mahaifinta: idan babu kyakkyawar muamula tsaianin uwarta da mahaifinta tabbas akwai matsala domin duk namijin kirki wajen neman aure yakan duba wannan domin diya taian samu training ne da mahairiyarta zai wahala pkaga diya batai halin uwarta ba masu kyau ko marasa kyau.
9. Kawayen Banza : duk budurwar kirki bazatayi kawanche da kawayen banzaba maza suna duba kawaye sosai domin muamula da kawayen banza kamar ka debi gawayi marar wutane kasakashi cikin mai wuta ahankali shima zai kama yazama mai wutar.
Daga karshe inso injawo hankalin yanmata cewa idan kina bukatar miji cikin sauki to kikama kanki kikasanche mai halaye nagari mai addini da girmama nagaba. Saboda tabbas maza nagari mai irin wannan halayen suke aura a matsayin mata.
Allah yazabawa kowa nagari Ameen
Duk wanda yasamu wannan sakon yayi kokarin sharing dinshi domin mutane dayawa zasu amfana insha Allah.