Ko Me Ke Kawo Shanyewar Tafin Sawu?
Shanyewar tafin sawu, wato "foot drop" a turance, yana faruwa ne sakamakon shanyewar ko raunin jijiyar laka da ke kaiwa da komowar saƙonni zuwa ga tsokokin da suke da alhakin ɗago tafin sawu da yatsu sama .
Wannan matsala ta shanyewar tafin sawu na kawo matsala musamman yayin tafiya da sauran matsalolin da suke faruwa tare.
Abubuwan da ke kawo shanyewar tafin sawu sun haÉ—a da:
1) Lahani ko raunata jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon matsalolin da ke biyo bayan tiyata, yanka, sara, suka ko haɗuran ababen-hawa, da sauransu.
2) Shanyewar É“arin jiki
3) Cutar shan-inna
4) Kuskurewar allura a ɗuwawu, musamman ga ƙananan yara.
5) Shaƙewa ko danne jijiyar laka ta sharaɓa sakamakon:
a) ɗaurin karaya a ƙafa, musamman ɗorin karaya na gargajiya ko kuma idan ba a sami kulawa daga likitocin fisiyo tun daga farko ba.
b) danne tushen jijiyar lakar a gadon baya sakamakon ciwon baya.
c) doguwar naƙuda, musamman idan aka samu tsawaitar zangon naƙuda na biyu, da dai sauransu.
Alamomin shanyewar tafin sawu:
1) Kasa iya ɗago tafin sawu sama; wannan zai sa mutum ya ɗinga jan ƙafa ko tafin sawu. Saboda haka, masu wannan matsala su kan yi tintiɓe, da kuma samun wahalar riƙe takalmi a ƙafar har sai an sanya maɗaurin agara.
2) Ciwo a tsokokin sharaɓa, wato gaban sangalali ko ƙwauri zuwa tafin sawu.
3) Jin yanayi marar daɗi a sharaɓa, misali, ka ji kamar tafiyar kiyashi ko dindiris a sharaɓa zuwa tafin sawu.
Wannan matsala ana warkewa sarai kamar ba a yi ba. Sai dai jinkirin zuwa asibiti na iya kawo nakasa a ƙafar. Saboda haka, akwai matuƙar buƙatar ganin likitocin fisiyo domin sune ke kula da farfaɗo da aikin jijiyar laka da tsokokin har aikinsu ya dawo yadda ya kamat