ABUBUWAN DA YA KAMATA MA'AURATA SUYI KAMIN SADUWAR JIMA’I
Idan dayanku zai je wa iyalinsa, ya kamata ya aika dan aike, wato ya kamata a ce kafin ya kwanta da matarsa su gabatar da duk wani wasa da zai motsa musu sha’awa, domin samun gamsuwar su kansu ma’auratan.
Sannan idan mutum ya sadu da matarsa, bai kamata ya yi gaggawar fitar da gabansa daga cikin matucinta ba har sai wannan matar ta sami gamsuwa daga gare shi, saboda wata matar ba ta samun gamsuwa a daidai lokacin da shi mijin ya sami gansuwa, har sai ya jira ita ma matar ta sami tata gamsuwar.
Wani mutumin ba ruwansa; da zarar ya sami gamsuwa da matarsa koda a iya wasan da su ke yi ne, to fa shi ya gama, ba ruwansa da ita. Shi ba abinsa ya yi ma sa zafi. Kun ga wannan shi ne karshen rashin adalci.
Wata matar kuma ta na da doguwar sha’awa, saboda haka, idan mijinta bai yi wasa da ita ba, sannnn bai jira ta samu gamsuwa daga gare shi ba, to maniyyin da ya ke jikinta ba zai sauko ya hadu da nasa ba, sai dai ya tsaya ma ta a mararta. Daga nan kuma sai ciwon mara, sai ciwon ciki, sai ciwon kai, sai warin gaba.
Daga nan sai mace ta dinga tsintar kanta da rashun kuzari da rashin walwala. Ta rasa abin da ya ke yi ma ta dadi, kuma wannan ke sa mace ta dinga jin haushin mijin da tsanar mijin. Sai ka ga mace ba ta girmama miji yadda ya kamata. A rasa dalili. Nan kuwa rashin ba ta hakkinta a shimfida ne ya jawo ma sa.
Sannan ya kamata mu sani cewar mata kala-kala ne kamar yadda maza su ke kala-kala. Akwai mai karfin sha’awa, wacce idan ba ta sami daidai ita ba, akwai damuwa. Sai dai ka ga auren ya na kai kawo. Karshe dai sai an rabu hankalinta zai kwanta. Ba yin ta ba ne; haka Allah Ya yi ta.
Haka su ma mazan, wani idan ya sami wata matar, da kanta za ta gudu. A-yi-a-yi ta dawo, ba za ta dawo ba, amma wata ta na kokari ta sanar da ’yan gidansu cewar ya fi karfinta.
Shawara ga mata da mazan da ba sa iya biya wa junan bukata; su sani ba sai ta kai su ga rabuwa ba. Idan ka san ba ka da juriyar da za ka iya biya wa matar ka bukata a shimfida ba, to ka dinga wasanni da ita sosai kafin ka shige ta, kuma ka tabbatar ka gane guraren da idan ka tattaba ma ta ta ke jin dadi sosai yadda kafin ku zo saduwa ka gama tayar ma ta da sha’awarta, ta fara jin dadi sosai.
Ka ga ka na shigar ta, kafin ka biya bukatarka, ta gama jin dadinta. Za ka ji ta sharkaf; komai ya yi daidai. Shawara ta biyu; ka kasance mai neman maganin karin karfin mazakuta da darin kuzari yadda matar taka za ta ji ka gagau.
Uwar gida idan mijinki ya na fama da rashin karfin mazakuta ko ba ya biya miki bukatarki a shimfida sai ki yi ma sa wannan hadin, ki samu:
– Bakin gagai
– Jan gagai
– Namijin goro
– Tsintsiyar maza
– Tatarida
– ’Ya’yan Dabino
– Citta mai yatsu
– Masoro
– Barkono
A hade, a dake su a tankade lukwui a dinga zuba ma sa a farfesu ko gasashshen nama ya na ci ko ki tafasa ma sa ki sa zuma ya dinga sha kamar shayi.