Domin mata 06
Folic acid Nau’i ne na vitamin B9, kuma yana daya daga cikin vitamin da aka narkar da shi a cikin ruwa (Water-Soluble Vitamins) wanda ake samu a cikin abinci da yawa, mafi mahimmanci daga cikinsu shi ne abinci mai ganye, kuma ana kera shi a matsayin kwaya.
Kwayar Folic acid ( Folic acid tablets) wassu kwayoyi kanana yellow mafi yawa yana zuwa da nauyi 5 (5mg).
Ana amfani da ita wajen magance karancin jajayen kwayoyin jini wanda rashin sinadaran iron ya kawo.
WADAN DA KE DA BUKATAR AMFANI DA FOLIC ACID:
1- Mata masu juna biyu
2- Mata masu shayarwa.
3- Masu ciwon cutar hanta.
4- Masu Ciwon Sikila.
MENENE HIKIMAR BAWA MATA MASU JUNA BIYU FOLIC ACID KO DA BASU DA MATSALAR KARANCIN JINI ?
Folic acid yana daya daga cikin muhimman sinadaran Vitamin da mata masu juna biyu suke bukata, sabida amfanin ta a jikin su.
Ga kadan daga cikin amfanin sinadaran Folic acid a jikin mata masu juna biyu:
Sati ukun farko na dan tayi a ciki , shine lokacin da wasu a kwayoyin halittarsa suke haduwa don Samar da ginshiki a kan yadda wasu sassa da kuma tsare-tsaren jikinsa za su kasance, saboda haka wannan lokaci ne mafi hadari a yadda gabansa za ta kasance ta yadda matsala a haduwar wasu kwayoyin halittar, za su sa ko da ya yi tsawon rai to zai rayu ne da matsala ta har ya mutu. To Folic acid yana taimakawa wajen haduwar wadannan halittun dai dai.
1- Birth defects : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yana bada kariya daga haihuwar yaro mai nakasa.
2- Folic acid deficiency: Yana kare mata masu juna biyu daga samun karancin sinadaran Folic acid.
Wanda karancin sa zai iya kawo matsalar:
- Zubewar ciki
- Na'uda kafin lokoci
- Mutuwar yaro a ciki
- Mutuwar Uwa.
3- Heart and blood vessel disease : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid suna taimaka wajen daidaita sinadaran homocysteine wanda hakan zai iya bada kariya ga cututtakan zuciya.
4- Cancer: Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yana iya rage hatsarin kamuwa da ciwon cancer.
5- Depression : Binciken masana ya nuna sinadaran Folic acid yakan iya taimaka wajen magance matsalar damuwa.
6- Dementia : Hakanan akoi kishin kishin na yana taimaka wajen bada kariya daga cutar kwakwalwa wanda yake saka mantuwa.
Wassu daga cikin amfanin ta:
- Yana Gyara fat
- Yana Gyara Gashi
- Yana saka cin Abinci
- Yana kare matsalolin jijiyoyi.
- Yana taimaka kula da kyakkyawan ƙwaƙwalwar ajiya.
Idan kinyi amfani da kwayar Folic acid yana kawo miki wadannan alamomi maza ki dakatar da ita sannan kije ga Likitan ki.
- Kaikayin jiki
- Kurajen Jiki
- Canza launin fata
- Rikewar Numfashi
Idan kana amfani da wadannan magunguna kada ki Kisha Folic acid sai kin shawar ci Likitan ki.
1- Anticonvulsants: Magungunan jijjiga kaman su fosphenytoin (Cerebyx), phenytoin (Dilantin, Phenytek), primidone (Mysoline).
2- Barbiturates : Magungunan da suke aiki a jijoyoyi wanda suke kai sako ga kwakwalwa.
2- Antimalarial: Magungunan cutar cizon sauro.
4- Methotrexate (Trexall): Magungunan da ake amfani da shi domin magance matsalar cancer.
Abinci Mai dauke da sinadaran Folic acid aciki :
1- Koren ganye da kayan lambu
2- Nama da Kifi
3- Wake
4- Hatsi
5- Dawa
5- Brown Shinkafa
6- Da sauran su.
Sai mun hadu a rubutu na gaba...