Amfanin Saka Kamfe (Pant) Ga ‘Ya Mace
1- Yana hana Kura shiga gabanKi wanda Ke haifar da warin gaba.
2- Yana hana busheWar gaba wanda Ke haifar da KaiKayin gaba.
3- Yana Kare mutuncin mace yayin da hadari ya sameta Ko Kuma al’adar ba zata ya sameta.
4- Ga mace mai yawan farin ruwa a gabanta (discharge) sa Pant yana rage yawan futowanshi.
ldan da hali zaiyi Kyau ya zama mace tana da Panties da yawa Kamar 12 Saboda idan nata ya jiKe sai ta dinga canzawa, idan Kuma babu hali Ko Kina ganin Wahalar haKan to sai Ki sami Karamin towel Ki aje a toilet dinKi duK sanda KiKa yi tsarKi sai Ki goge/tsane gabanKi da towel din Kafin Ki miKe tsaye Kinga batun jiKewar Pant
zai ragu.
HaKa Kuma anaso Mata su riKa amfani ne da farin Pant a ko yaushe Saboda yana Saurin taimaKa ma mace ta gane halin da gabanta ke ciki e.g colour discharge dinta ko unexPected menses zata zama alerted da wuri har ta dau mataKi.
Don Allah a Kula Ke da rabuwa da Pant Sai dai loKacin bacci. Ku koya wa yayanku yin haKan Domin ku mata ababe nKantau daraja kuma abin sha’awa amma ga wacce ta damu Kuma taKe Kulawa da Kanta.