Mijina Ba Ya Biya Min Bukata, Mece Ce Shawara?
Assalamun alaikum, Malam mace ce mijinta ba ya iya biya mata bukata saboda raunin mazakutarsa, kuma ashe abin da ya raba shi da uwargidansa kenan. Kasancewar ba ya biya mata bukata ta shiga cikin halin damuwa, sannan ta yanke shawarar cewa: in ya kira ta shimfidarsa ta daina zuwa, to malam ta yi laifi game da wannan shawarar da ta yanke?
Wa alaikum assalam. A shawarata kamata ya yi a kira magabatansu su zauna su tattauna a gano yadda za a warware matsalar. Idan har ya tabbata ba cikakken namiji ba ne to za a ba shi shekara daya ya nemo magani. Idan ya warke shikenan, in bai warke ba kuma za ta iya fadawa cikin haram idan ta ci gaba da zama da shi, to ya halatta a raba auran, kamar yadda aka raba da uwargidan.
Yana daga cikin manyan manufofin aure: ma’aurata guda biyu su katange junansu daga haram, in har aka rasa wannan to akwai matsala a zamantakewar aure.
Allah ne mafi sani.
MASU IRIN WANNAN MATSALAR SU NEMA MAGANI: