YIN ZINA DA BUDURWA KAFIN AUREKi daure ki karanta har karshe zaki samu ilimin rayuwa:SEX BEFORE MARRIAGE

YIN ZINA DA BUDURWA  KAFIN AURE
Ki daure ki karanta har karshe zaki samu ilimin rayuwa:

SEX BEFORE MARRIAGE 
Yana kula da al amuranki 
Yana kiranki a kodayaushe 
Shi mai yawan nemanki ne
Kodayaushe cikin yi miki alkawarin baxantaba iya rabuwa dake ba
Yayi alkawarin kasan cewa tare dake a kowanne irin yanayi 
Shi mutum ne nagari
Yayi miki alkawarin aure

INDA MATSALAR TAKE

Ya nemi da ki bashi kanki yayi zina dake
Kin tsorata da lafuzansa
Kin tsaya jinkiri kafin ki amince da bukatarsa

Amma daga baya sai kika amince domin kina gudun bacin ransa 
Kinyi tunanin shi mutum ne nagari 
Kinyi tunanin zai cika alkawarin da yayi miki

Ya ganki tsirara haihuwar uwarki 
Yayi zina dake 
Kin bashi abu mafi daraja da kima da kike alfahari dashi
Shikuma yakasance cikin gagarumin farinciki

KIN BASHI KANKI KAFIN AURE

Sai yafara neman karin yin zina dake dake akai akai 
Kin amince ya cigaba da kwanciya dake sau ba adadi
Sai kika fara ganin bakon sauyi daga gareshi

Ya fara nuna miki rashin kulawa kamar yadda yakeyi miki a baya 
Yafara daukar zafi da yi miki fada akan dan kankanin laifi

Yafara jifanki da munanan kalmomi aduk lokacin da kuka samu sabani
Yafara ganinki a matsayin yar takura a gareshi

Hhhmm

KINSAN DALILIN FARUWAR HAKAN?

 TO ZO KIJI

Saboda baki da wani abu na musamman da zaki bashi yaji kin birgeshi
Saboda baki da abinda zaiji yana dokinki 
Saboda yana ganin kinyi arha sosai a gareshi 

HABA YAR UWA ME KIKE TUNANI NE A BAYA?

Kina tsammanin zai cigaba da yin tattalinki ne alhalin baki da wani abu da zaki birgeshi dashi?
Kina tsammanin zai ga darajarki ne bayan kin zamo mace mafi arha a gurinsa?

Kina tsammanin ya cigaba da kasan cewa tare dake bayan ya kwanta dake  yayi zina dake
To dame kuma kike so ki kara birgeshi?

Da me kuma zakiyi alfahari a matsayinki na ya mace a idanunsa ?
Zai kara gaba ne ya barki ya cigaba da bibiyar sauran mata, 

Allah yasa mudace  Allah ya hadaku da masoya na gaskiya ba mazinata ba 

Allah yataimakemu yasa mudace da Alherinsa Aminu A

Post a Comment

Previous Post Next Post