AMFANIN GAWAYI WAJEN GYARAN LAFIYA DA KYAUTATA KAYAN AMFANIN GIDA.

AMFANIN GAWAYI WAJEN GYARAN LAFIYA DA KYAUTATA KAYAN AMFANIN GIDA. 
   Idan za a yi amfani da gawayi a dukkan fa'idojin da za mu ambata to ya kasance gawayi ne wanda aka yi girkin gida da shi ta hanyar ƙona itace. Idan kuma Gawayi ne wanda ake sayarwa wato (coal) to a fara yin girki da shi, ko a ƙona shi ya zama garwa shi sannan a kashe ai amfani da shi. 

AMFANIN GAWAYI.
 
1-  Cire wari
   Idan takalmanka suna wari; samu gawayi ka sanya ciki, ko kuma idan daki ne sai ka nemi wurin da yake warin ka jefa gawayi kawai zai daina, ko kuma idan firinji (fridge) ne cikin ke wari kawai jefa gawayi ciki zai daina. Saboda haka gawayi na dauke wari kowane iri ne in ya dame ka
 
2- Kashe guba. 
     Gawayi yana kashe gubar dake cikin abinci (kayan lambu)
 Al’umma kan koka kan yadda ake amfani da takin zamani ga abincin da muke nomawa musammam kayan lambu wanda sakamakon sa takin kan kasance kamar da guba a cikinsu. To kawai in ka samu irin wannan kayan lambun sanya gawayi ciki ka barshi zuwa safiya.
 
3- Maganin Ruɓa. 
    Gawayi yana taimaka wa abinci mai rubewa (kayan lambu) ya jima bai lalace ba.
 
4- Yana washe hakora su yi haske. 
 Idan kana son hakorinka ya yi haske, kar ka bata lokacinka wajen sauraron abin da masu tallan kayan wnke hokori, kawai samu gawayinka ka nika ya yi laushi. Sai ka sami hancin plantain (ayaba) ka rika tsomawa kana goge hakoran na tsawon mako guda.
 
5- Yana sake gyaran miyar da ta dauki lalacewa. 
      Idan miya ta dauki lalacewa in ta kwana da safiya kawai kar ki zubar, nemi gawayi ki jefa cikin miyar ki dora kan wuta ki dumama zai dawo da darajar miyar kamar da.
 
6- Yana rage karfin abin sha mai alamar bugarwa. 
    Duk abin sha mai dauke da gas idan ya kwana, in kana shakkar sha don wani abu da ka ji. Kawai tauna gawayi ka sa a ciki ka sha, an wuce wurin kenan.
 
7- Yana cire tsami a cikin kunun zaki. 
 Idan ba kya son kunun zakin da aka dama ya yi tsami mai ta da hankali, ta zarar an dama kunun sai a nemi gawayi a jefa ciki ya kwana zuwa safiya, lafiya lau ne.
 
8- Yana washe fuska da kuraje suka bata. 
     Kawai nika gawayi ki shafa a wurin. 
 
9- Yana busar da gyambo mai mugunya in aka nika aka sa garin aka barbaɗa. 
 
10- Yana taimakawa wajen kwantar da dattin cikin ruwa in aka jefa su ciki. 
 
 11- Idan cikinka ya kumbura shafa gawayi a kai zai sace cikin lokaci kalilan. 
 
12-  Yana cire dattin da ya kama jikin tiles a bayan gida ko dakin girki (kichen). Nika gawayi kiyi amfani da shi wajen cuɗe tayil ɗin. 
 
  Daga shafin Bashir Halilu.

Post a Comment

Previous Post Next Post