**Masha Allah**
**DAMBUN NAMAN KAZA**
Naman kazar turawa
Maggi
Man gyaɗa
Citt, kanumfari, tafarnauwa kidaka su
Bay leave
Thyme
Curry
Albasa
**Procedure"**
Dafarko bayan kinsa lemon tsami ko vinegar kinwanke namanki sekisa shi a tukunya kisa albasarki, dakakkar cittarki me tafarnauwa kisa bay leaves da dan kori da thyme se kayan dandano idan bakidasu ke kika sani 🙄,seki barshi ya dahu sosai karki cika ruwa sbd kajin Turai basuda kwari, idan ya dahu,seki sauke kibarshi yahuce karkifayi garaje dan kika ƙone ke kika sani 🤣,kizare ƙashin da fatar kibasu Safwan da haidar su cinye danke babu abinda zakiyi dasu tunda ga kazanan kinada ita, sekisaka a turmi kihigi fallen zani kisaki hanɗa da ganɗa kiyita daka eh nace kidaka har ya daku, seki kwashe
Anan suyar ta kasu kashi biyu
Taɗaya kisuba mai dayawa kamar zaki soya nama idan yayi zafi seki zuba namanki zakiga ya warware karki bashi yayi rumui sekisa kwando kitace yaɗan sha iska seki dauko abin tatar kokonki kizuba naman kimatse man yafita sarai zakiga yayi wara wara yayi gwanin kyau
Tabiyu kuma itace zakisa mai bada yawaba idan yayi zafi seki zuba namanki kiyita soyawa kina motsawa har yayi ja yasoyu shikenan
Note;
Suya ta farko tafi kyau da daukar hankali
Sannan abinda yasa nace kazar turawa sbd tafi tsoka sannan kazar hausa tafi dadi da fafesoo 😋😋 dakuma suya ko gashi sbd namanta yafi zaki kuma na kazar turawa yafi auki
Amma Duk wacce kikai da ita matsalarkice ke kika sani 🤣
Kowace tarubuta abinda takeso a koyar next post insha Allah wadanda sukafi yawa sune posting nagaba
Tags:
food