plantain and vegetables

PlANTAIN VEGETABLES RICE 

Kayan hadawa

🍝Tafashashshen shinkafa
🍝 Agada (plantain)
🍝 Karas
🍝Koren wake
🍝 Tattaruhu
🍝Tumatur
🍝Kayan kamshi
🍝Kayan dandano
🍝Mai ko butter
🍝Albasa
🍝 Nama (optional)

       YADDA ZAKI HADASHI

1. Dauko plantain naki ki yanka kanana ki barbada
gishiri kadan, sai ki daura mai a kan wuta ki
soya shi ki tsane. Ajiye a gefe.
2. Dauko tumatur, albasa ki gyara ki wanke ki
yanka kanana ajiye a gefe.
3. Daura tukunya akan wuta ki sa mai ko butter,
albasa ki soya sama sama sai ki kawo tarugu
kadan ki sa ki soya sama sama shima kawo
kayan kamshi, da maggi  ki sa
a ciki ki juya.
4. Sai ki kawo ruwan zafi ki sa (iya dai dai wanda
zai karasa dafa miki shinkafanki) sai ki rufe
nadan wani Lokacin har sai ya tafaso sai ki
kawo shinkafan ki sa ki juya sanna ki rufe
nadan wani lokacin har sai ya shanye ruwan.
5. Daga nan ki kawo karas, da koren wake (dama
kin dan tafasa su tare da baking powder) ki sa
ki juya ki barshi nadan wani lokaci daga karshe
sai ki kawo soyayyar agada, da yankakkiyar
albasa ki sa ki juya ki juya a hankali sai ki sauke SHIKENAN KINGAMA

NOTE : amfanin sah baking powder atafasa Koren wake da sauransu saboda kar kalansu yachanja ne

Post a Comment

Previous Post Next Post