AMFANI GUDA 10 NA MUSAMMAN DA KANKANA KE MA MAI CIKI

Kiwon lafiya
AMFANI GUDA 10 NA MUSAMMAN DA KANKANA KE MA MAI CIKI

 





Amfani 10 na kankana na musamman ga mata masu ciki:


Wannan karo mun nutsa cikin fagen kiwon lafiya inda mu ka kawo amfanin da kankana ta ke da shi ga mata masu ciki. Kusan dai kashi 90% na kankana ruwa ne don haka yake da amfani kwarai. Ga kadan daga cikin amfanin:



1. Mata masu ciki na yawan fama da zafin ciki da tashin zuciya don haka shan kankana na da amfani ga su masu juna biyu.



2. Kankana na rage yawan zufa watau gumi da masu ciki kan yi. Kankana na toshe jijiyoyi wanda hakan ke rage gumi da kuma kumburin jiki.

 


3. Ga matan da ke fama da zazzabin safiya, ruwan kankana na iya taimakawa wajen maganin wannan larura inji masana.




4. Kankana na da matukar amfani ga masu ciki musamman wadanda su ke fama da karancin ruwa a jikin su wanda yana iya sanadiyyar haihuwar bakwaini.



5. Masana sun ce kankana na iya maganin dabbare-dabbaren da fatan jikin mai ciki yake yi. Kankana na dai sa fatar mutum tayi kyau matuka.

 



6. Haka kuma masana sun ce kankana ta na gyara koda da kuma hanta wanda ke sa dattin da ke jikin mai juna biyu ya fita sarai.



7. Kankana na dauke da sinadaran bitamin irin su A, da B da kuma sinadaran potassium da magnesium wadanda ke kara karfi da kuzarin da mai ciki ke bukata.



8. Shan kankana na taimakawa wajen kara karfin sinadaran da ke yaki da cututtuka watau masu kare garkuwan jikin da mai ciki ke bukata.



9. Kankana na taimakawa mai ciki wajen kara karfi da kaifin idanun ta saboda karfin bitamin A kuma yana rage yawan kuraje a jiki.



10. A karshe ruwan kankana na kara kwarin kashin yaron da za a haifa saboda sinadaran da ke ciki irin su Calcium da sauran su.

Post a Comment

Previous Post Next Post