BAYANI AKAN TASIRIN AYA GA JIKIN DAN ADAM IN ANA CI KULLUMTasirin da Aya

BAYANI AKAN TASIRIN AYA GA JIKIN DAN ADAM IN ANA CI KULLUMTasirin da Aya keyi ga jikin Dan Adam idan aka yawaita cinta a kullum.
Ga wasu daga cikin amfanin sinadaran da aya ta kunsa:

- Tana dauke da sinadaran magnesium da calcium da kuma iron.




-Tana samarwa da jiki sinadarin protein da kuma lafiyayen kitse.





-Tana kunshe da sinadarin vitamin B wanda ya ke amfanar da fata da gashi da kuma farata.





- Don samarwa da jiki sinadaran vitamin da minerals, ya na da kyau a rika cin gram 70 zuwa 50 na Aya a kullum.






-Aya tana da amfani saboda tana kara karfin garkuwar jiki sinadarin carbohydrates.





-Ta yawan amfani da ita, za ka gano cewa kusan ba ka rashin lafiya kuma za ka ji dadi sosai.





-Aya na inganta yanayin da mutum ke ciki, tana tsawaita kuruciya, tana karfafa yanayin gudanar jini sannan tana kara kuzari na zahiri da na boye.





-Haka kuma aya tana da amfani ga sha'anin da ya shafi ciki da hanji, tana dauke da sinadarin da ke hana cushewar ciki da kuma kumburi.





-Aya na taimakawa wajen rage sinadarin kwalestaral (maikon cikin jini) mara kyau a cikin jini.

Post a Comment

Previous Post Next Post