Dabi'u guda goma da zasu tabbatar Maka cewa Kai Musulmin kirkine indai kana yinsu.
1) Zakaga kafi damuwa da sallah akan komai, zakaji bakada nitsuwa har sai kayi sallah, kuma zakaji sallah kamar jirgine dazai kaika wajen Allah cikin aminci da dacewa.
2) Zakaga kafi mutumta iyayenka akan kowa, sannan kuma kafi kyautata ma iyayenka akan kowa, sannan kuma zakaga sunfi kowa daraja a wajenka.
3) Zakaji damuwa idan baka da tsarki, sannan kuma zakaga kamar mutuwa zata riskeka idan baka kasance cikin tsarki ba.
4) Zakaji abinda kafi tunawa a rayuwarka shine mutuwa, sannan kuma bazakaji nitsuwa ba idan dare yayi har saikayiwa kanka hisabi kuma ka samu kanka cikin Alkhairanka sunfi yawa.
5) Zakaga kana kuka da kukan Al'ummah, kuma kana farin ciki da farin cikin marasa ƙarfi.
6) Zakaga kana tausayin wanda bayida sani, ma'ana wanda yakeyin abu cikin jahilci.
7) Zakaga mutanen banza suna ƙinka, mutanen kirki kuma suna sonka, sannan kuma mutanen banza suna daina magana idan suka ganka, mutanen kirki kuma suna ƙara ƙwazo idan suka ganka.
8) Zakaga kanason yaɗa sallama tsakanin mutane, sannan kuma zakaga kana sake fiska hatta ga Wanda baya ganinka (makaho).
9) Zakaga kafiso ka tsaya ma Halal komai kankantarsa, sannan kuma bakaso kaci haram komin ƙarancin sa.
10) Zakaga bakaso kayi saika tambaya umarnin Allah ne, kokuma umarnin Manzon sa, sannan kuma baka amfani da ra'ayin kanka.
Ya Allah duk wanda ya yaɗa wannan karatun ka yaɗa sunanshi a mafi girman Aljannah (fir'daus), Ameen Ya Rabb