LABARI MAI RATSA ZUCIYA MAI TAKEN DAREN DA BAZAN TABA IYA MANTAWA BA!IDAN KANA DA AURE KO KINA DA AURE DON ALLAH KA KARANTA ZAI FADAKAR DA KAI 😭

LABARI MAI RATSA ZUCIYA MAI TAKEN DAREN DA BAZAN TABA IYA MANTAWA BA!

IDAN KANA DA AURE KO KINA DA AURE DON ALLAH KA KARANTA ZAI FADAKAR DA KAI 😭

Abokina yau ranan uku da rasuwar mata ta wanda Baffa ya takura min ya sa na aure ta a bisa tilas, amma bari kaji irin abin da ya faru tsakanin mu.

 Idan tayi aikin gida bansan ko sannu nace mata ba sai dai kullum burina naga kuskuren ta anan zakaga saurin mitata.

Hakanan ban san iya adadin kukanta ba Haka nake shareta na kwanta bacci na.

Sai dai ita mai tsoron Allah ce koda munyi fada takan bani hakkina.

Baxan bata haquri ko lallabi ba sai dai na juyo in kalle ta wani lokacin tana kuka haka zan karbi hakkina😭

Idan ta tashi tun asuba 4am tafara nafila har sai 7am take tashi.

Zanji ta tashi don gyara gida da karyawa. Zan tarar da komai wanda nake bukata na karyawa inajin dadin hakan amma girman kai bai barni nace mata koda sannu ba sai dai ma nayi mata kallon banza. 

Ya zamto ni mai rufin asiri ne amma ban san nayi mata kyauta ta kudi ba Alhalin nafi kowa sanin tana bukatar hakan, sannan tana da mahaifiya amma na kasa ganewa zata iya saya mata wani abu.
Saboda bata da Sana'a, aiki kuma daman na hana, Ko canji bana bar mata agida saina kwashe kayana😭

Tana girmama iyayena, yan'uwana Hatta ga jikoki ita Mai son kyauta ce Amma batada halin yi. Idan ko ta samu kudi to tabbas zatayi alkhairi dasu. Tinda na aureta ban damu da yi mata sutura ba gani nake ai tanada na auren mu.

Tana ciwo(rashin lafiya)amma bakina bai taba cewa ya jiki kona damu da hakan ba. Sai dai naji tanata juyawa amman saboda Mita na da sanin kar raina ya canza haka zata haqura.

In kayan aikin abinci ne tace a sayi wani abu gani nakeyi kamar taimakon ta nakeyi. Gashi ni bana son kyautar abinci.....itako mai alkhairi ce.

Idan gaban yan'uwa nane ko magana tamin dakyar nake amsawa. Duk wannan ukuba bata taba kai qarana ga iyayena ko nata ba.Sai dai naji tana mana Addu'ar fatan alkhairi tare da zaman lafiya cikin sujjada tana kuka😭

Ranar da bazan manta ba itace:

Watarana Ta tambayeni zata wunin sallah gidansu, Na amince mata. Haka ta hada komai nata ta gyara tun dare tamin Abinci tamin lunch ta ajje taima yaron mu khaleel wanka. Sai naji sallama.

Ashe qanwar tace da addanta suka zo Dan inada mota Amma sun san bazan kaita ba. Domin Gani nake daukar ta ciki ma alfarma ce. Suka gaidani na amsa..... suka wuce dakinta tafito tace abban khaleel zamu tafi.

Budar bakina nace bazaki jeba, da sauri ta dago ta kalleni, nace eh. Tayi roqon duniya nace a'a haka ta share hawayen ta ....... A tunanina zata fadima yan'uwa ta. Sai ta shige daki tana rusa kuka. 😭😭😭

Na kasa zama nazo bakin kofa naji tana addua kamar haka

"Ya Allah nidai ban sabeka wajen hidimar biki naba😭. Banyi abunda da ka Hana na kidi ko rawa ko hada mata da maxa ba😭.Ya Allah ka karkato da hankalin miji na zuwa gareni ya Allah karka bani damar fushi da mijina,Sai ta fito wajen 'yan uwan tan.

Sai na labe ji nayi tace adda kuyi haquri abban khaleel baiji dadi ba. Bazan samu zuwa gida ba haka sukayi addua Allah ya bani lafiya suka wuce. Na sake binsu naji qanwar ta tace anya ba hanata yayi ba adda?

Da shike sun samu tarbiya sai Yar tace AA baijin dadi da kin ganshi.. amman nasan tagane.

Na koma daki na tarar tana kuka mai ratsa zuciya tabbas na karaya😭. Amman sai naga ta tashi na dauka fada zamuyi. Sai naga ta shiga toilet tadan dade kafin ta fito nasan kuka take.

Sai ta fito ta daura sallah al'adar tace dama yin walaha. Na fita falo domin nima raina ya sosu yau, Amma girman kai bazai barni na bata haquri ba.

Sai naji tana fadin " Ya Ubangiji nayi dukkan addu'an da ake lokacin daren farko bayan daura aure na.
Nashiga gidana da sallama da addua. Nayi adduar zama bakin gadona. Duka tana Fadi cikin kuka😭😭

Ya Allah ina roqon ka idan na saba maka cikin rashin sani ka yafeni..

Ya Allah karka kama mijina wlh na yafe masa. Ina kuka ne domin neman gafarar ka badan fushi dashi ba😭👏🏻

Ya Allah nasan shima bazai so kunci naba saide jarrabawa. Ya Allah kasa mijina ya gyara😭 Kayi albarka gareshi
Da arziqin sa. Yaa Allah kada ka kamani da rashin kyautawa iyayena bani da abinda zan saya musu kona ziyarar cesu saida yardar mijina".

Tabbas ranar naji tausayi na tuna duk kunci da take ciki da wulaqanci nine na saka ta. Ashe ma addu'a take min in tana kuka ban sani ba.Nayi nadama amman girman kai ya jani. Na shirya Zan fita sai na samu tana kwance nace zan fita......

Haka ta daure tamin addua na lura kamar daqyar ta miqe amma na share. Na fice sai tace min inajin zazzabi abban khaleel, Cikin murya mai rauni:

Nace Allah ya sauwaqa kisha magani mana nasa kai na wuce abuna. Cikin dare
Ina kwance domin banzo dakinta ba tunda na dawo, Ashe wannan ciwon zazzabi yaci karfin ta
Na sameta Kwance kan sallaya. Nace yau bazaki zo dakina bane? Wai a tunani na tazo ta bani hakki na ni namanta ma tana zazzabi Bata amsa ba,
Nace bada ke nake ba A tunani na ko fushi tayi.

Haushi ya kamani naje da nufn jawota. Nan naga tashin hankali DAREN DA BA ZAN TABA MANTAWA BA....sai naga ta fado qasa......na duba da kyau ashe ta rasu tana sallah kan sallaya ta jingina da kujera😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭😭 Nayi kuka kamar raina zai futa nayi dana sani babu adadi ashe haka nake sonta girman kai ne ya hana nake bata kulawa kaico na 😭😭🤦‍♂️🤦‍♂️🤦‍♂️

Nayi da nasani kuma nayi rashin matar kirki 😫😭

Mece ce shawarar ku akaina 😩😭😫


✍️ *~Kwasauri gariii🥳~*

Post a Comment

Previous Post Next Post