Yadda zakiyi amfani da ruwan shinkafa wajen gyaran Fuska da jiki, da Kuma anti - aging.
Mata barkan mu da wannan lokaci, da fatan kuna nan cikin koshin lafiya. A wannan lokaci ga wani albishir na kawo muku! Ko kun san cewa ruwan shinkafa yana dauke da sinadaran gyaran fatar jiki hade da haskaka hammata?
Idan kin kasance mai zubar da ruwan shinkafa ne bayan an tafasa, ya kamata a daina domin ruwan ba karamin amfani yake da shi a fatar jiki ba. Don haka ne a yau na kawo muku yadda za a yi amfani da ruwan shinkafa wajen gyara fatar jiki. Ruwan shinkafa yana sanya fata sheki da haske da kuma warkar da cututtukar fata da dama domin za a iya amfani da shi a kowace irin fata.
• Domin goge kwalliyar fuska: A tafasa shinkafa sannan a tace ruwanta a bari ya huce sannan a zuba nono ko madara kadan a ciki sannan a samu auduga a rika dangwala ana goge kwalliyar fuskar, yin hakan na sanya fatar fuska laushi da sheki.
• Hasken fata: Bayan an tafasa ruwan shinkafa an bari ya huce, sai a rika yin wanka da ruwan ko kuma a wanke fuska da ita domin sanya hasken fata.
• Ruwan shinkafa yana dauke da sinadaran kare illar da rana ke yi ga fata don haka yana magance kodewar fuska da kuma kare fuska da fatar jiki daga kodewar rana.
• Wanke fuska da ruwan shinkafa na warkar da cutar kyasbi. A rika wanke fuska da ruwan shinkafa wadda take da kauri domin magance cutar kyasbi.
• Amfani da ruwan shinkafa na warkar da matsalolin kurajen fuska ko kaikayin fata sannan yana taimakawa wajen sanya fata sulbi.
• A samu zuma da kurkum a kwaba sannan a zuba ruwan shinkafa kadan a shafa a fuska a jira ya bushe na tsawon minti talatin kafin a wanke. Yin hakan na rage shekaru da rage tsufar fata sannan yana sanya fata sulbi da sheki.
• Idan an tafasa ruwan shinkafa, a jira ya huce sannan a shafa ruwan mai kauri a fuska bayan ya huce, sannan a murza kamar dilke sannan a wanke, yin haka na sanya fata sulbi.