Duk wata ya'mace wadda tasan ciwon kan ta bata da wani babban buri kamar ta ganta a dakin mijinta, gidan aure rufin asirine kuma security ne ga rayuwar ya mace uwa uba kuma darajar ya mace shine gidan mijinta,,,,,
Yanzu An wayi gari wai har gori a keyi wa wadda batai aure ba, ana ganin kamar laifin tane wata tambayar ma har da gatsali a cikin ta da izgilanci da zallar rashin tauhidi
wannan tambayar babu ma lissafi a cikin ta ko kadan, sbd duk san auren mace wllh bazata dauki kanta da kanta tayiwa kanta aure ba har takai kanta dakin miji,,,, idan kince mata taki aure shin ke ki fara tambayar kan ki, shin kece kika aurar dakan ki?? sayo miki mijin a kayi a kasuwa?? ko kuma kyau ne ko girman iko ne yasa ki kayi aure?? in dai har baki da amsar wannan tambayoyin tabbas baki da lasisin fadawa wata wannan kalmar wato "kinki aure" idan kuma har da gaskene kina so tayi aure tsakaninki da Allah, dan Allah kibata mijin ki ta aura,,har ❤️ta buga ko 🤣,,,to in har bazaki iya bata mijinki ta aura ba yaka mata kidaina yi mata wannan tambayar wadda itama batada amsar ta,,, ya kamata ki gane cewa shi Aure lokaci ne wllh idan lokaci yayi babu fashiiii, shi aure nufine na Allah keda ki kayi auran ba wayanki ne ko dabarar kice tabaki ba lokacin kine yayi sbd idan kika duba za kiga tsala2n yan'mata ga kyau ga diri ga komai yanzu sune suke gidan iyayan su sbd lokacin su bai yiba,,,,
🍃sbd haka ya kamata ki gane cewa Aure nufi ne na Allah tambayar wata taki aure/yaushe zatayi aure banaki bane👌 kamata yayi ki mata Addua Ya Allah kabawa duk wadda batai aure ba miji nagari, sbd baki fita san kiga tayi aure ba, tafiki jin zafin hakan A zuciyar ta sbd haka idan bazaki tayata da addua ba gara kiyi🤐yafi Alkhairi, sbd bazaki iya yi mata maganin matsalarta ba Abu daya zaki iya taimaka mata dashi wato addua
🧕Yan'mata ku kwantar da hankalin ku Allah yana sane daku wllh da yawa jinkiri Alkhairine nasan Abun babu dadi amma hakurin shine mafita.