kowane burin da namiji shine Allah ya hadashi da mace tagari,
mace tagari ita ce wanda ko kadan kyalkyalin abubuwan duniya baya gabanta burin ta ace tasamu lahiran ta.
Mace tagari ita ce wanda mijin ta idan ya kalle ta zaiji nishadi,yana kuma alfaharin samun ta a matsayin matar sa.
Mace tagari ita ce mai rufawa mijin ta asiri
mace tagari ita ce mai tausayawa mijinta.
Mace tagari ita ce mai tarbiyyar da yaranta akan hanyar gaskiya,ta yadda duk inda yaran ta suka shiga zasu zama abin sha'awa acikin mutane.
Mace tagari ita ce mai kishin mijinta kishin gaskiya,bawai kishin hauka da wasu matan ke yi ba.
Mace tagari ita ce mai amfani da iliminta gun amfani dashi
mace tagari ko kadan bata yarda tayi munafurcin mutum.
Mace tagari ita ce mai kare dukiyar mijin ta.
Mace tagari ita ce mai biyayya ga mijinta .
Mace tagari ita ce mai zama da mijin ta akowane irin yanayi yake ciki.
Mace tagari takanyi imani da Allah ,a koda yaushe zuciyar ta cike yake da imani da kuma tsoron Allah.
©️ Nusaiba Tasiu Abdulrahim