WACECE MACE TA GARI?Bauta dai shine dukkan abun da Allah Ya ke so, kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.

WACECE MACE TA GARI?

Bauta dai shine dukkan abun da Allah Ya ke so, kuma Ya yarda da shi na daga zance da aiki.

Kuma duk mace ta gari zaka same ta da ibada, wato mai dagewa ce wurin bautar Ubangijinta. Sannan tana tsoron Allah da qanqan da kai gare Sa.
Kuma ta aminta tun daga farkon auren ta cewa aure ibada ne, kuma Sunnah ne mai qarfi zata raya. Kuma duk abun da take yi a cikin gidan ta tana da lada. Idan mace ta sa haka a ranta abubuwa da yawa a rayuwar aure za su zo mata da sauqi.

Ita ce mai dogaro ga Allah a cikin dukkan al’amuran ta. Kuma tana komawa gare shi a lokacin yalwa da lokacin tsanani. Kuma tana godiya gare Shi a cikin ko wane hali.

Mace ta gari sam bata wasa da sallolin ta biyar a gidan ta. Kuma ba a barin ta a baya wato tana tashi cikin dare ta roqi alkhairan duniya da lahira.

Tana qoqarin yin azumin nafila tare da izinin mijin ta.

Tana qoqarin yin kyauta da sadaqa.

Tana dagewa wurin yin addu’a. Duk abun da ya same ta na rayuwa to ta kan tsananta roqo.

Mai yawan ambaton Allah ce da Istigfari. Bakin ta danye yake wurin ambaton Allah. Ba ashar da maganganu marasa amfani ba.

Tana yin biyayya ga mijinta, idan har umurnin sa bai sabawa Mahalicci ba.

Kuma tana dagewa da sauran ibadodi na samun lada.

In ba ku manta ba Annabi (SAW) ya faďa a hadisi:

((إِذَا صَلَّتِ الْمَرْأَةُ خَمْسَهَا، وَصَامَتْ شَهْرَهَا، وَحَفِظَتْ فَرْجَهَا، وَأَطَاعَتْ زَوْجَهَا، قِيلَ لَهَا: ادْخُلِي الْجَنَّةَ مِنْ أَيِّ أَبْوَابِ الْجَنَّةِ شِئْتِ)). [رواه أحمد].

“Idan mace ta yi sallolin ta biyar, ta yi azumin ramadan, ta kuma kiyaye farjin ta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, sai a ce da ita: “Ki shiga aljannah daga qofar da ki ka gadama daga cikin qofofin Aljannah”. [Ahmad].

Babu yanda za a yi a kira ki ta gari, bayan kina tsallake sallah, wato yin sallah yana miki wahala.

Inaa! Mace ta gari ta miki nisa, don ita rige-rige take wajen ganin ta kusanci Mahaliccin ta da ibada.

✍️ Zainab Auwal Musa

Post a Comment

Previous Post Next Post