BAN AUROKI DON NA YI WASA DA KE BA

BAN AUROKI DON NA YI WASA DA KE BA

Sunyi aure bayan soyayya da sukayi abar kwatance, bayan sati biyu da auren, Angon ya tashi daga bacci domin ya shirya xuwa wajen aiki, sai ya nufi bandaki domin ya wanke fuskarshi, shigarshi keda wuya sai ya dubi madubi ya kalli fuskarshi kaca-kaca da zane na janbaki kala daban-daban. 
Amaryar tashi yarinyace danya, kuma gata da kyaun hali. Yana bacci tayimar kwalliya, Kuma ta yi mai hakan ne da nufin  nuna wasa irinna masoya, domin su yi dariya idan gari ya waye. 
Mijin ya wanke fuskar tashi cikin fushi, ya nufi kitchen domin shan shayi kamar yadda ya saba kowacce safiya. Bai samu shayin ba, sai Kuma fushin ya qaru, ya nufi kanta. 
Tayi murmushi ta dauka cewa zaiyi mata dariya, sannan ya fada mata wassu romantic words. Sai tayi karo da akasin hakan inda ya talleta da mari sai da ta xube kasa, sannan Kuma ya hauta da bala'i yace da ita: "ban auroki don nayi wasa dake ba, ni ba qaramin yaro bane, na aurokine don mu samu xuriya nazamto mutum cikakke a idanun Al'umma.
Shin kinason kiyi irin rayuwar dakike karantawa a littatafan soyayya ne da fina-finai? Idan zaki farka ki farka, wadannan abubuwa dakuke gani a film ko littatafan novels basa gina gida, basa samarda abinci, basa renon yara. Kuma ina sanar dake yau zan gayyato abokaina xuwa lunch gidannan, inason ki shirya mana komai kafin nadawo,  kin fahimceni kam?"  
 •
Yafice waje ya barta cikin kuka tanata haki, shi Kuma garan yana kallon kanshi a matsayin jarumi maigida. 
Hakan daya mata ya sanyata rashin lafiya. Ammana dukda hakan tayi sauri ta nufi kitchen taje tana kuka tanamar girkin.  
Mijin bayan yafita sai ya gamu da wani abokinshi yana bashi labarin abinda yafaru yana dariya yana cewa dashi: "Wai sun dauka aure kawai love and romance ne. Hakan danawa yarinyar nan haka yakamata ake yiwa mata, idanba haka ba bazata koyi darasi ba. 
Sai Kuma akaci sa'a abokin nashi ba irinshi bane, baima barshi ya kammala bashi labarin ba, sai ya katse shi yace dashi: "bawan Allah kai wani irin mutum ne?  Menene yasa kazamto mugu ga matar ka? Shin hakan miji nagari yakamata ya zamto? Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yana cewa: "ku kula da mata, su mata kamar glass suke. Dole ka tsawata musu, ammana Ka zamto mai taushin rai gateau, kada kuma ku fasa xukatansu". 
Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam yakara cewa: "Wannan duniya wajen zamane na wucin gadi, Kuma mafi jin dadin zaman duniya shine mutum yasamu mace tagari. 
Kayi hankali da kalamanka dakayi na cewa: "girki da renon yara". Ba dole bane tayi maka wadannan, ammana kyautatawarka gareta zai sanyata tayi maka wadannan abubuwa harma fiyeda hakan basai ka fada mata ba. Yakamata kasani ba yar aiki bace gareka.  Ka koma cikin hankalinka mana abokina, ka tuba xuwa ga Allah. Ka koma ga matarka ka bata haquri kada Kuma ka sake sanyata fushi". 
Mijin sai yadawo cikin hankalinshi yaji haushin abinda ya aikata, sai yayi dana-sanin abinda yayi. Sai ya yanke hukuncin kiranta ya sanar da ita cewa ya fasa xuwa da abokanshi lunch din, tayi musu nasu su kadai kawai. Ya kira waya tayi ringing ammana ba'a dauka ba.... 
Sai yayi maza ya nufi gida, yaje ya kwankwasa kofa nanma babu wanda ya amsa. Lokacin dazai fita ashe yabar keys dinshi a gida saboda yafita cikin fushi. Yana tsaye sai wayarshi tayi ringing. 
Ashe yayan matarshi ya kirashi. Matar tashi ta kira yayanta yazo ya kaita asibiti yayinda taji batada lafiya sosai sanadiyyar bakin cikin da Mijin nata ya sanyata. 
Sai yayan matar nashi yace dashi: "Brother muna asibiti.". Muryar tashi alamun yana cikin fushi, wanda hakan ya sanya Mijin nata xuciyarshi ta kada, sannan yaji tsoron kada wani abu yasamu matar nashi. Sai ya tari aca6a yanufi asibiti inda ya tarar da duk yan gidan su matar nashi a asibitin.
Kowanne cikinsu fuskokinsu a dare suna jiran fitowan likita daga kanta. Yayi tunanin zasuyi fushi dashi, ammana Kuma sai yaga kamar basuma san abinda yafaru ba. Yayi musu sallama sannan ya jira likitan shima yaji meye zaice. 
Bayan wassu mintuna, saiga likita yafito daga dakin da aka shigar da ita ya tarar dasu sannan yace dasu: "Inna lillahi wa inna Ilaihirrajiun, Allah Ya mata rahama, xuciyarta ta riga ta buga kafin a kowata garemu". 
Kowannensu sai suka fashe da kuka musamman ma mijin. Yayi nadama ya kuma zargi kanshi. 
Mahaifiyarta ita tayi mata sutura akan sallaceta a wannan ranar. Da yammaci, Mijin ya kar6i keys a wajen yayan matar nashi yadawo gida.
Ya shigo gida ya tarar da dinning table dinsu a rufe. Ya bude yadin data rufe table din sai ya tarar da abincin dayafi qauna an dafa an ajiye akan table din, sai kuma yaga wata paper a liqe a jikin fridge dinsu anyi rubutu kamar haka: "my love kayi haquri ka yafemin domin naso na kunyataka ta hanyar yimaka abinda ba al'adarku ba, ka yafemin domin nayi zaton abinda na maka zai sanyaka kayi dariya sannan ka rungumeni kace dani kana Qaunata.
Ka yafemin domin halin yarinta da nayi maka, na dauka zaka daukeni tamka yarinya karama ba babbar mata ba sa'arka. Nayi maka alqawari bazan sake sanyaka fushi ba ko 6ata maka rai, ina fatan abokanka zasuji dadin wannan girki danayi maka, I love you so much my hubby".
Sai ya kalli table din, sannan ya watsar da dukkanin abincin dake kai, ya zauna yanata sharan kuka yana cewa: "meye nayi miki masoyiyata, na kashe ki da bakin xuciyata, ki yafemin". 
Yan'uwa masu hankali da tunani, a wannan zamanin namu mukan kaskantar da duk wani mutum dayake nuna soyayya da Kuma sakalta matarshi sosai. 
Muna mantawa da cewa zaka zamto mutum ne nagartacce matuqar ka zamto mai tausayin matarka, Kuma hakan umurnine na Ubangiji Subhanahu wa Ta'ala. 
Allahu Jalla wa Azza Ya na cewa: "Wamin ayatihi an khalaqa lakum min anfusikum azwajan litaskunoo ilayha waja'ala baynakum mawaddatan warahmatan inna fi zalika laayatin liqawmin yatafakkaroon". 
Mu tuna cewa matarka daga gareka take, idan tana farin ciki, zakayi rayuwa mai nagarta.  
Mu tuna cewa domin gina gida nagartacce, dole sai anyi haquri, Gaskiya da Kuma nuna so da qauna. 
=
=
Allah Ya mana jagora. Aameen
©Copied

Post a Comment

Previous Post Next Post