Kwalliya

Kwalliya 

BUDURWA ko BAZAWARA dukkan wacce tayi mafarkin tana yin kwalliya ko ana mata kwalliya koma hakanan kawai taga kwalliya ajikin ta bata san lokacin data yi ba DUKA ana maki bushara ne da samun miji ne nagartacce/nagari Wanda zaya kula da dukkan lamuran ki baki iyawar shi MUSAMMAN idan dama kina addu'ar samun miji managarci/nagari 
Miji nagartacce ba dole sai mai kudi ba, inaga duka mun san abinda ake jibantawa da nagartacce/managarci/nagari 

AMMA idan namiji yayi mafarkin yana yin kwalliya ko an mashi kwalliya koma hakanan kawai yaga kwalliya ajikin shi tayi kyau toh mai yiwuwa dama Dan gwagwarmaya ne toh ana mashi inkari ne da samun abinda yake gwagwarmayan dmn shi MA'ana dai zaya cimma abinda yake nema, kama daga neman aiki, neman jari, neman aure, da dai makamantan su 

Hakazalika idan mace mai ciki tayi mafarkin ana mata kwalliya ko tayi koma hakan kawai taga kwalliya mai kyau ajikin ta ko fuskarta haihuwan MACE ne zata yi insha'Allah

IDAN KUMA mace mai aure wacce suke zaman rashin dadi da mijin ta sai tayi mafarki irin wnn ana bushara ne cewa zata samu aminci da mijin ta wannan rashin zama lapian zaya wuce insha'Allah 

Ganin kayi kwalliya Amma sai ta lalace ko wani ya lalata maka/ki toh da yiwuwar akwai wani lamari da ka/ke son cimma yake baka wahala Kuma gaskiya ba lallai ne ka samu ba face bacin Rai zaka shiga akan abun

ALLAH SHINE MAFI SANI

Post a Comment

Previous Post Next Post