SIRRIN HADA DILKA:

SIRRIN HADA DILKA: 

Akwai tazara me yawa tsakanin mace me kula da jikinta fiyeda wanda bata mayarda hankali akayi, wannan bawai sai yan mata ba, harda matar aure koda yake da yawa mata suna damuwa da gyaran jiki da fuska da duk wani shafe shafe don ayi fari a yayinda suke yan mata, amma bayan anyi aure suna ganin hakan bashida wani fa,ida amma kuwa akwai amfani hakan domin kula da jikinki shine zaisa ki zama tamkar sa'ar yaranki, 
A wannan yanayin fata tanayin kaushi tarinka tauyewa dole 
mata suna bukatar sabulun wanka kona shafawa ajiki domin zama cikin laushin fata da dumi wanda shine ake fadawa hadin DILKA & HALWA asalin yar DUBAI anayiwa amarya kwana3 kafin aurenta, sannan koda kinada aure zaki iya amma dai ya zama bakya fita rana sosai, hadin sabulun shine wanda akeyi da (zuma) (lemon tsami) (dilka) (garin zaitun) (kurkur) (sugar) (man kwakwa) sune zasu goge duk wani tabo da wani tauyewar fata jiki yayi laushi kana yayi haske, amma kafin muje ga yanda ake hadashi bari muje ga asalin inda aka samo irin wadannan kayan gyaran jikin

A kasar India da akwai wani waje me suna shimla wanda ke Himachal Pradesh, an tabbatar anan ne aka fara 
duk wani hadi me kara hasken fata wanda akeyi da itatuwa, kasancewar yanda mutanen wannan yanki suka aminta da duk wani gyaran jiki wanda ke mayarda mace karama a koda yaushe ana ganinta kamar bata tsufa, hakan yasa suka samu daukaka wajen hada manyan sabulai da ake shiga kasar dubai dasu wanda ta hakane al'ummar kasashen afurka suma suka shiga cikin jerin mutanenda ke aiki da kayan itatuwa wajen gyaran jiki, wanda ayanzu anan kasar ma ya zagaya ko ina, yanzu ya zama tsofon yayi amfanida mayikan turarwa wajen gyaran jiki, domin irin wadannan sune suke gyara fata babu ruwanki da narkanwa,

Ana samun sugar kama cocali uku azuba akan wani abu da za'a iya dorawa akan wuta, sai akunna masa wuta saiya fara darkewa yana danko sai asaukeshi a zuba zuma fara da kurkur sai dilka da garin zaitun duka yawansu daya, sai amatsa lemon tsami da man kwakwa kadan, sai acakudashi sosai sannan ana gogashi ajiki duka inda akeso a gyara, yanada danko idan kiga goga sai a dayeshi sannan a bari yayi mintuna talatin sai ayi wanka da ruwan dumi.

Post a Comment

Previous Post Next Post