Mace ta gari ƴar soyayya ce kuma tana sadaukar da dukkan soyayyan ta ga mijinta.
Ita ce mai wasa da dariya da miji, wato tana soyantar da mijin ta son ta, kuma tana sanya shi dariya da jin daɗi in suna tare.
Ba ta nesantar sa in yana gida tana nan nane da shi a jikinta kamar mage, kuma ta sabar masa da jikinta. Sannan ba ta rabo da taɓan sa da sunbatar jikinsa dss kin dai gane ai.
Ita ce mai koyo kallolin soyayya da abun da zai sa mijinta ya ji daɗin zamantakewa da ita, wato bata bari soyayyan ta ya zama outdated kullum tana upgrading soyayyan ta da levels din ta don burgesa. Har mijin ta ya ji kai ita ce ɗaya tamkar da dubu.
Idan baya gida sauri sauri ya ke yi ya dawo gare ta, saboda idan ya kalle ta zai samu farin ciki da nutsuwa, kuma yana baƙin cikin nesantar ta.
Ita ce take sanya gidan sa ya zama wani kwarya-kwaryan Aljannah da zai samu farin ciki da kwanciyar hankali a ciki a duniya.
Kuma tana kawar da duk wani abun da zai kawo masa baƙin ciki da ɓacin rai, kuma tana nemo nau’ukan wasa da labarai da za su saka shi jin daɗi da nishaɗi.
Mace ta gari soyayyan ta ya kan sa namiji ya ga duk wata mace ai ba ta kai tashi ba, hakan sai ya ba shi kariya daga kalle-kallen matan waje. Kuma in ma zai ƙara aure zai yi ne ba wai don ke kin gaza masa ko kin dai na burge shi ba, a’a sai don raya sunnar ma’aiki (SAW).
Mace ta gari mijin ta babu shi babu zaman majalisa, saboda yana da majalisan babban birnin tarayyan soyayyar ki a gidan sa. Domin yana shiga gida matar sa za ta cika shi da kalolin soyayya to me zai zauna a waje yayi?
©️ Zainab Auwal Musa