Matashi Don Mene Ne Kakeson Yin Aure ????

Matashi Don Mene Ne Kakeson Yin Aure ????

—Daga Ibrahim Y. Ibrahim

Aure abu ne mai kyau domin sunnar Manzon Allah (S) ne. Daɗin daɗawa muna ƙara godiya ga Allah ta’ala da yaba iyayenmu ikon haifemu ta hanyar Aure ba ta hanyar Zina ba‚ Allah ka tsare mu da faɗawa ga wannan hallaka. Ya kai matashi mai son yin Aure! Akan mene ne kakeson yin Auren? Da za a tara matasa a ƙalla mutum 1000 a masu wannan tambayar 850 cikin mutum 1000 ɗin nan. Amsar da za su bayar shi ne; Ina son nayi Aure ne domin na Huta da yin wanki‚ sannan zan kwanta a sabon katifa ga mayafi mai ɗimi‚ gashi zan huta da sayan abinci‚ za ta rinƙa dafawa‚ kuma zanzo da abokai muci abinci‚ sannan ga daren farko da zan raya sunna‚ sa an nan zansha magani kala-kala domin sai nayi sau kaza don Inason ta haihu da wuri‚ da dai sauran dalilai daban-daban da wasu daga cikin Matasa suke son suga sunyi Aure.

Na’am bance ka cire hakan a Zuciyarka ba‚ amma kasan da cewa matarka sunanta matarka ba baiwa bace‚ kuma kasan ita ɗin wurin samun Natsuwarka ne‚ sannan ita kaɗaice Allah ya yarje ma ka ka kusanceta yayin da kayi kanason biyan buƙatan ka‚ kuma ka samu lada in kabi yadda shri’a ta koyar. Ya kai matashi mai son yin Aure‚ ka taɓa yin wannan tunanin? Ya ya za ayi in nayi Aure na kula da karatunta matata? Ya ya za ayi in nayi Aure na kula da addinin matata? Ya ya za ayi in nayi Aure na kula da yanayin mutanen da matata take huɗɗa dasu? Ya ya za ayi in nayi Aure nayi ƙoƙarin biyan buƙatun matata na yau da kullum? Ya ya za ayi na kula da ƴan ƙananun haƙƙoƙin matata? Ya ya za ayi naba matata kulawa fiye da mahaifinta? Shin wai ina da hankalin da zan riƙe mace da suna Aure? Shin ina da hanyoyin samun 5/10? Shin in nayi Auren nasan akwai iya ranakun da ake aikata Sunna ɗin? 

Shin nasan akwai addu’o‚in da ake karantawa in za a aikata sunnar? Shin in zan aikata sunnar nasan ƙa’idojin da addini  Musulunci ya tanadar? Shin in matata ta Haihu ina tunanin ya ya za ayi na ba yaro/yarinyar tarbiya da ilimi domin na sauke haƙƙi

Post a Comment

Previous Post Next Post