GANYEN GWANDA DA YAYANSA A MAGUNGUNAN GARGAJIYA NA KASAR SIN

GANYEN GWANDA DA YAYANSA A MAGUNGUNAN GARGAJIYA  NA KASAR SIN 

Sharadin Shine Ayi Sharing 🔔🔔🔔

Kamar yadda Hausawa ke cewa  saniya Nagge jikinta babu na yarwa, haka lamarin yake dangane da bishiyar GWANDA  Sinawa na  ce mata ita ma babu abin yarwa a jikinta domin dukkanta daga yayan (seeds) da ganyen  da  dan  da ake sha duk suna da matukar magani a jikin dan’adam wanda duk binciken ikitocin kasar Sin ya tabbatar da hakan kuma suna amfani da su sosai. Ga kadan daga cikin magungunan gargajiya da ake yi da GWANDA.

1. DANGUE FEVER. Wannan wani irin zazzabi ne da  wani nau’in sauro ke haddasawa amma ban a Malaria ba. Idan irin wannan sauro ya ciji mutum yana matukar rage masa wasu sinadarai a cikin jininsa wanda ke matukar illa har. Akan dafa ganyen gwanda a sha wanda nan take ke dawo da wannan sinadarin kuma mutum ya sami lafiya. Wannan sinadari shi ake kira (PLATELET)

2. MALARIA.  Zazzabin cizon sauro irin wanda aka saba da shi a nan wurarenmu.  A kan jika ganyen gwanda ko a dafa a sha  ,yana matukar maganin Malaria.  Domin a cikin ganyen akwai sinadarin da ake kira ACETOGENIN wanda ke saurin kasha kwayoyin cutar malaria kuma ana iya shan gayen a matsayin maganin kare kai daga kamuwa da cutar ta Malaria.

3.  Shi gwandan da kansa da kuma ruwan ganyen gwanda maganine sosaai na cutar hanta, yawan shansa yana warkar da cututtuka iri daban daban na hanta. Yana kuma maganin shawara.

4. KUMBURIN CIKI. Shan gwanda  ga wanda yake yawan samun kumburin ciki  yana taimakwa sosai domin yakan sake ciki wato yana hana (constipation

5. ULCER.   Haka kuma yana maganin ULCER sosai musamman ULCER na ciki.

6. CUTAR SUGA .( diabetes) idan ana dafa ganyen gwanda ana sha ko ana nika yayan gwanda (seeds) ana sha, yana saukar da yawan suga da ke  cikin jinni sosai. Kuna yawan shansa na maganin wasu matsalolin koda da yawan kitse a jikin hanta.

7. CIWON AL’ADAR  MATA.  Mata masu zafin mara ko jin ciwo lokacin al’adarsu ko yawan ciwon ciki, yawan shan ruwan ganyen gwanda yana da matukar amfani wajen kawo karshen wanan matsalar, kuma yana daidaita kwanakin al’ada na mata cikin sauri.  Ana dafa ganyen sai a tace  a dan sa masa gishiri a cikin ruwan da garin TAMARIND sai a gauraywa a glass na ruwa a dafa, wannan take yake kawar da zafin ku murda na al’ada.

8. LAFIYAR FATAN JIKI. Shan ganyen gwanda yana  sanya fatar jiki ya kara laushi da haske kuma ya kawar da cututtukan da ka iya samun fatan jikin mutum. Domin yakan kawar da kwayoyin cutan da ke karkashin fata.

9. MAGANIN SANKO DA ZUBEWAR GASHI. Shan ruwan ganyen gwanda yana maganin sanko sosai da kuma yawan zubewar gashin kai, yana kuma sanya gashi ya kara baki

10. MAgANIN CUTAR CANCER/DAJI.yawaita shan ganyen gwanda na maganin cutar cancer/daji sosai musamman cancer na mama da na huhu  da na hanta da saifa. Hka kuma na maganin kumbirin sassa daban daban na jikin dan’adam. Wadanda ake musu CHEMOTHERAY, shan ruwan gwanda na rage matsalolin da ke tattare da wannan nau’I na jinya.
Idand ruwan ganyen gwanda yana maka daci ko hamami, kana iya gauraya shi da ruwan kwakwa domin ya baka dandano mai kyau. 
Allah sa mu dace . 

 (Yana da kyau ka tuntubi likitanka kafin ka soma amfani da kowane irin magani}  Mu kwana nan. Allah sa mu dace.

Post a Comment

Previous Post Next Post