KUSKUREN DAKE SAKA MATA SAMUN

KUSKUREN DAKE SAKA MATA SAMUN INFECTION NA FITSARA (UTI)
Kusancin dake akwai tsakanin anal opening( inda kashi ke fitowa) da vaginal opening( inda macce ke fitsari da al'ada) shi ke saka sauri da kuma sauqin samun damar qwayoyin cuta shiga daga anal opening zuwa vaginal opening idan macce tazo wanke kashi. Alhamdulillah, musulunci yayi tanadi, shi tsalki akan fara tsalke mafitsara ne, ayi tsarkin fitsari sannan ayi na kashin. Muna iya cewa daga gaba zuwa baya kenan. Inda duk macce tazama batasan hakan ba, tau sai anyita samun matsalar UTI (infection na mafitsara) saboda zatazo tace a ha'de zata wanke kashin da fitsarin anan qwayoyin cutan zasu Samu shiga suyi cikin Mafitsaran, wasu lokutan har a cikin qoda su illata qodan. Wannan fa basai ga balagaggar macce ba, hatta jarirrai haka yakamata ayi musu tsalki kosu UTI yakan kamasu. Allah yasa Ku gyara Ku kuma kiyaye. Ku maza kun huta baku cika samun wannan ta tsalki ba, saboda ramukan baa kusa suke ba. Sai idan mutum sakaci yayi.

Post a Comment

Previous Post Next Post