FA IDA GA ME JUNA BIYU🪷

🪷FA IDA GA ME JUNA BIYU🪷
9- Naqarshe...gudumawa tabiyu da zaki bawa danki...daga zarar ance zaki fara shayar dashi...kina jinin biki....daure kitashi kidauri Alwalah...Kifara bashi Nono na dama kafun kisa abakinsa kice bismillahi Awwalihi wa Akirihi...sai kisamishi Abaki...a wnn lokaci karkiyi surutu kiyita masa addu a gwargwadon yanda zaki iya...harsai yagama shaa..donshine shansa na farko...
Idan zaki bar yaronki shi kadai adaki kunna masa karatun Alqu ani ko Ruqiyya.. a wayanki ki ajiye agefenshi.... 
Duk Abunda kikeyi mangariba nayi dauki danki kigoyeshi yaji dumin jikinki harsai magriba yawuce ki sauqeshi ko kibawa yayunsa su goyashi...
tsara lokacin shayar da danki bawai kowani kuka yayi ki danna masa nono Abaki ba...wani kuka Qila cikinsa ke ciwo...wani zaiyi fitsari ne...wani qila yayi bayan gidane yake damunsa yanaso kicire masa...wani yagaji da kwanciyan gefe dayane sai kimasa miqa ki juya shi kigyara masa kwanciya....
snn kada kina bawa yaro nono kikwantar dashi....qila nonon Bai sauqa cikinshi ba...zai dawo dashi ta hanci ta baki😳
kina gama bashi sashi akafadanki ki kwantar kina shafa bayansa a hankali...zakiji yayi gyatsa😊sai ki kwantar..
yan uwa anan zan taqaita badon matakan tarbiya da reno sun Qare ba suna nan dayawa sosai....
Amma iyaye musani mu muke fara bata yaranmu tun suna qanana...Don da daga kin haifesa zaki fara bashi tarbiyaa...Allah ya shirya mana yaranmu yabamu ikon basu tarbiyya ta addini..Subhanakallahumma wabihamdika Ash hadu An la ilaha illah anta astagfirukallahumma wa a tubu ilaika🥰🥰

Post a Comment

Previous Post Next Post