AMFANIN GURJIYA A CIKIN JIKIN DAN ADAM ( BAMBARA BEANS )

AMFANIN GURJIYA A CIKIN JIKIN DAN ADAM ( BAMBARA BEANS  )

kamar duk abinci mai wadatar furotin shine ( thermogenic ) kuma yana taimakawa wajen sarrafa nauyi. yana ɗaukar lokaci mai tsawo don narkewa kuma jiki yana amfani don ƙarin kuzari dan narkar da shi. Wannan zai iya taimaka maka rasa nauyi yayi da kake samun gamsuwa da sauri kuma ka ji Ka koshi na tsawon lokaci kuma ka sha ruwa mai yawa.

Shin Gurjiya Tana da amfani ga ciwon sukari?

Sakamakon wannan binciken ya nuna cewa Gurjiya yana da fa'ida mai mahimmanci ga lafiya Haka nan zai iya zama mai matukar taimako wajen sarrafa ciwon sukari, kiba da cututtukan zuciya da ke tasowa daga ( hyperglycemia )

Shin Gurjiya tana da amfani ga koda?
Gurjiya na iya inganta aikin koda . 

Har ila yau, Gurjiya Ta ƙunshi ma'adanai masu yawa na magnesium, wanda ke da mahimmanci Ga Koda.

Gujiya wata kwayar tsaba ce wadda Mutanan Afrika suke amfani da ita Wadda take da matukar muhimmanci a jikin dan’adam. Awani bincike da wani Masani yayi, ya ce gujjiya tana taimakawa jiki kamar haka: 

1. A cikinta akwai sinadarin carbohydrate 65% akwai sinadarin protein 18%.
 2. Kwayar ta akwai dandano Mai dadi Sosai idan ana ci.
 3. Tana taimakawa jiki Wajan narkar da abinci.
 4. Tana da Sinadarin ( micronutrien.)
 5. Tana Taimakawa jini wajan gudana a jikin dan’adam. 
6. Tana Taimakawa garkuwan jiki wajan yakar cutar kansa. 
7. Sannan tana kare mutum daga kamuwa da cutar kwashoko. 8. Tana karawa kashin Mutum karfi da nagarta. ( Calcium )
9. Tana saka karancin cholostrol. 
10.Tana taimakawa jiki wajen kare shi daga ( arthritis )
11. Tana taimakawa mutum wajan hanashi gudawa da kuma dakile gudawa a lokacin da ake yinta

Post a Comment

Previous Post Next Post