MAGANIN TARI NA YARA MAI TSANANIDaga shafin Magungunan Musulunci

MAGANIN TARI NA YARA MAI TSANANI

Daga shafin Magungunan Musulunci

Wannan tambaya ne da wani dan uwa turo zuwa ga wannan shafi ranar 29 ga watan 9 ga tambayar kamar haka

Dan Allah ka taimake ni da maganin tari na yara tarin na da tsanani

Tari mai tsanani abune da ke sanya mutum ya gaji lokaci guda saboda yawan amfani da energy damutum ke yi lokacin tarin, yana iya janyo ciwon kai , ciwon kirji,yana hana yin barci da sauransu

Idan yaro ko babba na fama da wannan lalura sai abi wadannan hanyoyi don magance wannan lalura kamar haka

~A samu manyan farin alabsa a guda 2 a dafa shi da ruwa kofi 2 bayan ya dahu sai a tsiyaye asa zuma asa a sake dafawa don ya yi kauri sai a sauke a barshi ya yi sanyi ana shan cikin cokali 1bayan anci abinci har na wata 2 wannan babban mutum ma zai iya yi amma shi babban cokali zai yi amfani da shi ba karami ba

~A samo garin hulba da garin habbatus sauda'a da man tafarnuwa da zuma a hade su guri guda ana sha wannan yana da tasiri sosai

~A dafa tafarnuwa da lemon tsami dan kadan da zuma cokali 1 ana sha kullum safe da yamma

~A rika shan ruwan kahl rabin karamin cokali bayan kowane awa 3 amma babban mutum sai ya sha karamin cokali shima bayan koowane awa 3

~A rika dafa hulba ana sha tare da zuma kullum sau 3 a rana

Abni lura Hulba na da tasiri sosai wajen magani tari kamar yadda Ibnul Kayyim ya fada a cikin littafinsa mai albarka DIBBUN NABAWI

Alla ka kara mana lafiya

Post a Comment

Previous Post Next Post